Wata tsohuwar mata mai suna Daljinder Kaur, ta haifi danta na fari, a ranar 19 ga watan Afirilu 2016, a Arewacin Haryana, bayan auren su da kusan shekara 50 ita da mijinta mai suna Mohinder Singh Gill.
Tsohuwar da mijin ta sun nuna godiya ga Allah da samun dan nasu

Matar da mijinta, wadda ta haihu a wani asibitin iyalai, dake Hariyana, sun karbi dan nasu cikin farin ciki, inda suke cewa,
” Muna cike da murna da farin ciki, ganin cewa yau muna dauke da dan mu, na cikin mu da muka haifa.”
Anurag Bishnoi, wanda shine likitan dake gudanar da asibitin da matar ta haihu, ya bayyana cewa,
“da farko, sun fara dar-dar akan ko matar bazata iya rainon cikin ba duba da yawan shekarun ta, amma daga baya bayan anyi mata gwaje-gwaje, sai suka tabbatar da cewa zata iya rainon cikin”
Yanzu na ke jina cikakkiyar mutum
Cikin farin ciki, tsohuwar mahaifiyar tace, har yanzu bata makara ba wajen zama uwa ga dan jaririn nata wanda shine danta na fari a duniya, inda tace yanzu ne take jin cewa ta cika mutum.
” Allah ya karbi addu’ar mu, yanzu ne nake jin cewa na cika mutum, da kai na nake kula da dana, ina ji na cike da kuzari. Miji na, mutum ne mai matukar kula da kuma taimaka mini a koda yaushe “
Kaur din take fada wa kafar labarai ta AFP dake arewacin birnin Amritsar
Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal
Tsohuwar jarumar Kannywood wacce ta dade a masana’antar inda ta kai fiye da shekaru 20 da suka gabata tana fim ta ce har yanzu ba a dena yayinsu ba.
A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, ta fara da bayar da tarihinta inda ta ce an haifeta a garin Katsina inda ta tayi ta yi karatu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com