Wata mata da basu dade da yin aure ba, ta kashe mijin ta, ta hanyar banka masa wuta, sannan ita ma ta kashe kanta.
Dalilin da yasa ta kashe mijin nata

Matar wadda aka bayyana a matsayin Ife, ta kashe mijin nata mai suna Bolu ne saboda, tace yana cin amanar ta, inda ta rubuta wani sako a manhajar watsof din ta, inda tace, a sakamakon kaita bango da yayi, to yau kafin faduwar rana za’a fasa kukan duka su biyun.

Bolu din wanda yana zaune ne a Cairo, amma ya kan ziyararci Najeriya, ta kone shi ne a cikin gidan sa, inda ta hada da shi da dukiyar sa.
Matar ta kashe kanta bayan ta babbake mijin nata
Bayan Ife din ta gudu ne sai aka ruga da Bolu din zuwa asibiti.Rahotanni sun nuna cewa, daga baya an gano gawar Ife din, wacce ake zargin ita ce ta kashe kanta.
Shima Bolu, daga baya yace ga garin ku nan, a sakamakon kunan da ya mamaye mafi yawan sassan jikin sa.
Budurwa ta kashe kanta bayan an wallafa bidiyon ta na tsiraici a shafukan sadarwa
A ƙasar Egypt wato Masar wata matashiyar budurwa ta halaka kan ta har lahira bayan hotunan tsiraicin ta sun karaɗe shafukan sada zumunta.
Tuni ƴan sanda suka damƙe wasu matasa guda biyu bisa zargin su da sa hannu dumu-dumu fcikin lamarin bayan mutuwar matashiyar yarinyar.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com