Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar, yace komai dangane da rayuwar sa, ciki har da zaman sa shugaban ƙasa a mulkin soja da farar hula, tsautsayi ne.
Obasanjo, wanda tsohon shugaban mulkin soji ne an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a mulkin farar hula a shekarar 1999, yace zaɓin shi na zama manomi ne kaɗai ba tsautsayi ba.
Yana alfahari a kira shi da manomi
Jaridar The Punch ta rahoto cewa da yake magana a wata hira da Segun Odegbami a gidan rediyon Eagles7 Sports 103.7 FM, a birnin Abeokuta, Obasanjo yace ina alfaharin a kira shi da manomi.
Komai da nayi a rayuwa ta tsautsayi ne. Noma ne kawai abinda nayi wanda ba tsautsayi bane.
Kasan tasowa ta. An haife ni na taso a ƙauye. Naje makaranta bisa tsautsayi. Mahaifina yace ba zaka yi wani abu daban ba? Kawai sai na faɗa harkar noma.
Obasanjo ya shawarci matasan Najeriya
Sannan kuma, Obasanjo ya shawarci matasan Najeriya da su karɓi ragamar shugaban a halin yanzu.
Obasanjo yace kada matasa su yarda wani ya riƙa kiran su da shugabannin gobe, inda yake cewa goben ba tabbacin zuwan ta.
Obasanjo yace wasu gurɓatattun shugabanni za su lalata goben da ake cewa idan har matasa basu tashi tsaye suka ɗauki goben su a hannun su ba.
Yace:
Shawara ta ga matasan Najeriya itace, kada ku yarda wani yace muku kune shugabannin gobe. Idan kuka jira zuwan goben nan kafin ku amshi ragamar shugabanci, wannan goben ba tabbacin zuwan ta. Za su lalata ta.
Yanzu ne lokacin, matasa ku tashi tsaye don ganin hakan ya faru.
Najeriya na buƙatar shugabanni masu matsanancin hauka – Obasanjo
A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana irin shugabannin da Najeriya ke buƙata.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Najeriya tana buƙatar shugaba dan gada-gada, wanda kuma yake da hauka, domin ya saisaita wa kasar zama tare da dora ta a saiti.
Tsohon shugaban ƙasar, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar Shugabancin kasa, a karkashin jami’yyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, a gidan sa dake Abeokuta, a jihar Ogun. Obasanjo yace, shi kansa wasu abubuwan da suka shafi Najeriya, sai da yayi su kamar a haukace, kuma baya neman afuwa akan hakan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com