29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dangane da fim din batsa, Mama Daso ta yi martani

LabaraiKannywoodDangane da fim din batsa, Mama Daso ta yi martani

Wani yanki daga cikin shirin fim din Gurnani da wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta ta TikTok, Nura Nabala ya wallafa ya yi matukar daukar hankulan jama’a, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

A bidiyon anga inda jarumi Salisu S Fulani ya bukaci Mama Daso a matsayin ‘yar aikin gidansu da ta siyo masa fim da mujallar batsa tare da sanar da ita yadda zata yi sumogal dinsu ya amsa.

Bayan ganin wannan bidiyon ne aka dinga yada shi ana ta maganganu marasa kyau wanda akasari mutane sun koka ne akan yada fasadi da kuma koyawa yara rashin tarbiyya.

Jaruma Saratu Gidado, wacce ta kasance a cikin shirin ta yi martani ga wata ma’abociyar TikTok mai suna Leematu, wacce tayi tsokaci karkashin bidiyon inda tace:

“Wannan su ne masu koya tarbiyya?

“Eh sun koya mana kuwa Alhamdulillah amma kallar fim naku ma yana taka rawa.”

Daga nan Saratu Gidado ta mayar mata da martani inda tace:

“Wa ya matsa muku dole ku kalla?”

Leematu ta bata amsa da cewa:

“Kiyi hakuri, ni bana kallon fina-finan Hausa wallahi. Ni bazan iya cacar baki da ke ba saboda kin isa haifar kama ta. Kiyi hakuri.”

Take Daso ta kara bata amsa da cewa:

“Ba tarbiyya muke koyarwa ba, iyayenku ya kamata su koya muku tarbiyya, mu sana’a muke yi.”

Anan ne wani Young Alaji ya ba Daso da martani inda yace:

“Allah wadaran naka ya lalace, indai wannan ne irin taku sana’ar, Allah wadarai dai. Domin lallai wannan yana daga cikin yada alfasha.”

Wannan ba shi ne karon farkon da ‘yan fim da su ke bayyana cewa sana’a su ke yi ba koyar da tarbiyya ba, akwai wata hira aka yi da Shehu Hassan Kano, inda yace nishadantarwa suke yi.

Mama Daso ta je gaban kotu, ta ce sai Deliget sun fito mata da kudinta da su ka lamushe

Jaruma Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Mama Daso, ta yi bidiyo gaban babbar kotu da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano, kamar yadda ta sanya a shafinta na Facebook.

Kamar yadda ta shaida, Delegate din da su ka lamushe mata kudi ba tare da zabenta ba za ta kai kara saboda yadda su ka ci amanarta.

Ta bayyana cewa kudinta ba zai ciyu ba, za ta shiga ciki don yankar sammacin da za a kai musu gidajensu, kuma ta ce Yakubu Muhammad ne shugabansu wanda ya gabatar da su a wurinta.

Ta ci gaba da cewa:

“Ba a ci min kudi a kwana lafiya, ban ci kudin kowa ba, ba wanda zai ci kudina. Ga ni a kotu ina shaida wa jama’a, duniya ta sani, don ban ci nanin ba, nanin ba za ta ci ni ba.

“Ina gaya muku a fito min da kudina. In ba haka ba a ji kiran alkali. Ga ni nazo zan yanki sammaci, yanzu zan shiga. In ana taba kudin wasu banda nawa. Gara a kiyaye.”

Ta bayyana cewa ba ta yafiya, babu wanda zai ci kudinta ya zauna lafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe