25.1 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

2023: Shettima ba zai kunyata ƴan Najeriya ba -Buhari

Labarai2023: Shettima ba zai kunyata ƴan Najeriya ba -Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace Kashim Shettima, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ba zai ba ƴan Najeriya kunya ba idan jam’iyyar ta lashe zaɓen 2023.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wurin wani taro da jiga-jigan jam’iyyar APC wanda aka gudanar a faɗar shugaban ƙasa. Jaridar The Cable ta rahoto

Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa; Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi; da Idris Wase, mataimakin shugaban majalisar wakilai, na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

Buhari na ganin cewa Shettima ba zai ba ƴan Najeriya kunya ba

A wata sanarwa daga Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Buhari yace tsohon gwamnan na jihar Borno ba zai ba ƴan Najeriya kunya ba.

Ya yabawa ƴaƴan jam’iyyar APC


Shugaban ƙasan kuma ya godewa ƴaƴan jam’iyyar saboda ƙoƙarin su wurin tabbatar da cewa babban taron jam’iyyar da zaɓukan fitar da gwani sun gudana cikin nasara.

Ina son nuna godiya ta gare ku kan rawar da kuka taka yayin shirye-shiryen, na farko babban taron mu na farkon shekara, sannan daga bisani kuma zaɓukan fitar da gwani. Inji Buhari

Dukkan ku kuna da zuciya ɗaya, wurin son abinda yafi kyau ga jam’iyya, inda aka samar da ɗan takara cikin sahihin zaɓe.

A garemu gabaɗaya, aiki tare da haɗin kan jam’iyya shine abinda yafi muhimmanci, sannan sai buri ya zo na biyu. Naji daɗi kun fahimci hakan maimakon biyewa son zuciya.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa jam’iyyar saboda wayar da kan ƴan Najeriya musamman matasa su yi katin zaɓe.

Katobarar kalami guda 3 marasa dadi da Buhari ya gwabawa ‘yan Nageriya kuma ko a jikin sa

A baya-bayan nan shugaban kasa Buhari, yana yin wadansu kalami da wasu yan Nageriya ke ganin kamar ma izgilanci yake yi musu ganin cewa ya taho gangarar mulkin sa. 

Kalaman shugaban, wadanda wasu ke ganin tamkar ma wasan yara yake yi ko tazo mu ji ta, suna harzuka da yawan yan Nageriya, saboda rashin kangado da kuma karancin taushi da kalaman ke dauke da shi. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe