29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bayan mutuwar aurenta, Rahama Hassan ta bi sahun Rahama Sadau

LabaraiKannywoodBayan mutuwar aurenta, Rahama Hassan ta bi sahun Rahama Sadau

A yadda lamurra suke wakana, a cikin kaf masana’antar Kannywood babu wata jarumar da ta kai jaruma Rahama Sadau samun caccaka musamman kan yadda take wallafa hotuna da bidiyoyi wadanda take rabar maza, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ba anan ta tsaya ba, tana yin shiga wacce ke fitar da tsiraicinta, wanda saboda haka yanzu haka ko ta yi makamancin abubuwan nan mutane sun dena mamaki ko kuma surutai akai.

Sai dai rashin damuwa da cakuduwa da mazar da take yi yana da alaka da shiga cikin jaruman Nollywood wadanda yawancinsu ba hausawa bane kuma ba musulmai ba.

Sannan akasarinsu ba ‘yan arewa bane don haka basu dauki dafa mace a komai ba don al’adunsu ba su hana su yin hakan ba.

Bayyanar wasu hotuna na jaruma Rahama Hassan rungume da wasu jarumai da mawakan kudu ya dauki hankula, duba da yadda duk da haramcin hakan a addinance da kuma al’ada ta zage tana ta hotuna a cakude cikinsu.

An ganta rungume da jarumi Gentle Jack wanda aka fi dani da Vuga, da wasu kuma rungume da mawakin Zule Zuu a wani taron wata kungiyar da ke da’awar hadin kan Najeriya (AVCIN).

Jaruma Rahama Hasan ta yi matukar taka rawa a masana’antar Kannywood tun daga shekarar 2011 zuwa 2015, inda ta fito a fina-finai da dama kamar Birnin Masoya, Madubin Dubawa, Lamiraj, Wasan Maza, Zarar Bunu, Wata Rayuwa da sauransu.

Ta auri wani dan siyasa mai suna Usman Elkudan a shekarar 2017, wanda Allah ya yi ma auren mutuwa a shekarar nan inda aka fara ganinta a masana’antar.

Masoyan jarumar ba su ji dadin ganinta a yanayin ba, musamman bayan an gan ta a tawagar 13 times 13, sai dai ganinta da wadannan ‘yan kudun zai fi bata musu rai.

Muna fatan Ubangiji ya yafe mata tare da ganar da ita ya kuma sa ta kara samun wani mijin tayi aure. Ameen.

Auren Rahama Hassan ya mutu, ta dawo harkar Kannywood

Wani bidiyo ya fara yawa a shafukan sada zumuntar zamani wanda fitaccen furodusa, Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa ya dauki hankulan mutane da dama.

A bidiyon, wanda Tashar Tsakar Gida ta nuna, an ga tsohuwar jarumar tare da sauran jarumai sanye da hula ta kungiyar mawaka da jarumai ta 13 X 13, inda mai shaddan ya rubuta “Rahama Hassan is back” ma’ana “Rahama Hassan ta dawo”.

Wannan bidiyon ne ya kara bayar da tabbacin cewa auren Rahama Hassan ya mutu saboda babu yadda za ayi da aurenta ta dawo fim har su kai ga yin tsayuwae gab da gab da MaiShadda.

Musamman idan mutum ya kalli yadda jarumar ta dakata da yin fina-finai tun kafin ta yi aure har ta kai ga yin aure.

Ko a shafukan sada zumunta ba a fiye jin ta ba sai jefi-jefi.

Bayyanar Rahama Hassan a daidai lokacin da ‘yan fim suke ta aure ya janyo surutai inda wasu suke cewa dama ko sun yi aure ba sa son zama.

Dama tun a bayan an fi bayar da misalin masu zaman aure kamar ita jaruma Rahama Hassan din, Mansura Isah, Maijidda Abdulkadir, Wasila da sauran su.

Duk da dai akwai wasu jaruman da auren su yake mutuwa amma basa dawowa fim wanda hakan yake sa asirin su ya rufu.

Duk da dai ana cewa aure rai gare shi, ana samun mutuwar aure a cikin mutane amma na ‘yan fim ya fi bayyana kasancewar su sanannun mutane ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe