27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Katobarar kalami guda 3 marasa dadi da Buhari ya gwabawa ‘yan Nageriya kuma ko a jikin sa

LabaraiKatobarar kalami guda 3 marasa dadi da Buhari ya gwabawa 'yan Nageriya kuma ko a jikin sa

A baya-bayan nan shugaban kasa Buhari, yana yin wadansu kalami da wasu yan Nageriya ke ganin kamar ma izgilanci yake yi musu ganin cewa ya taho gangarar mulkin sa. 

Kalaman shugaban, wadanda wasu ke ganin tamkar ma wasan yara yake yi ko tazo mu ji ta, suna harzuka da yawan yan Nageriya, saboda rashin kangado da kuma karancin taushi da kalaman ke dauke da shi. 

kalami
Katobarar kalami guda 3 marasa dadi da Buhari ya gwabawa ‘yan Nageriya kuma ko a jikin sa

Kalami na farko da ya fusata yan Najeriya, shine

“wanda shugaban yace, zai bar kasar Najeriya fiye da yadda ya karbi mulkin ta”. 

Hakika wannan Kalami, ya bata ran da yawan yan Najeriya, wanda wadansu, suke ganin cewa, yana nufin akasin abin da ya fada ne, ma’ana zai barta a halin tabarbarewa ne fiye da yadda ya same ta. 

Kalami na biyu a jerin kalaman shine, inda shugaban yace

” Na Kagara da na bar mulkin Nageriya na koma Daura. ” 

Wannan Kalami ma ya fusata yan Nageriya, inda mutane da dama ke ganin, ajiye mulkin ya kamata yayi a maimakon fadar cewa ya Kagara ya gama. 

Masana, sun yi sharhi akan maganganun shugaban, inda wani masani mai suna Dr Yahaya Getso, ya kira kalmin shugaban da abun kunya, tatsuniya da kuma wasan yara. 

A cewar wannan masani,

” Farko dai idan aka kalli yanayin kasar ta fuskar tattalin arziki, za’a ga cewa gwamnatin Buharin ba da gaske take yi ba, tunda ta kasa samar da yanayi mai kyau tare da dukkanin kayan aikin da za’a yaki rashin tsaron. 

“Sunce sun kashe makudan kudade akan tsaro, amma har yanzu babu tsaron sai tsoro. Makin da za’a iya baiwa Buhari akan tsaro shine 15 cikin 100, idan aka kwatanta shi da makwaftan kasashen da yake magana akan su. 

“Ta fuskar cin hanci da rashawa kuwa, babu wani abun kuzo mu gani da suka tabuka duk da kururuwar da suke yi cewa suna dakile cin hanci, har yanzu babu mutum daya da aka ga sun hukunta akan hakan. 

Kalami na uku wanda shima ya tayar da kura

Shine shugaban ya fada, a lokacin da yaje garin su daura bikin sallah. Inda yace,

” Da ‘yan Nageriya sun san irin halin matsin tattalin arzikin da wasu kasashen Africa suke ciki, da, su sai su godewa Allah “. 

Babu shakka wannan Kalami na Shugaba Muhammadu Buhari, ya bata ran yan Najeriya. 

A cikin masharhanta a kan wannan Kalami, akwai wani mai suna Muhammad Auwalu Jarimi, wanda yace,

“Kowanne tsuntsu kukan gidan su yake yi, shima da ya san matsin rayuwa da yan Nageriya suke ciki , to da bai fadi wannan magana ba. Mun dora duk matsalar yan Najeriya a kansa, domin shi yace zai iya, ta karba, da yaga ba zai iyaba sai ya sauka, ya baiwa wanda, zai iya”

shi kuwa wani masani mai suna Dr.Ibrahim Muhammad, shugaban sashen tsimi da tanadi na jamia’ar Dutse, ya dora abin ne akan doron ilimi da kididdiga inda yace,

“Idan ana so a gane abin da shugaban ya fada gaskiya ne ko ak asin haka , to sai aduba abu uku . Na farko tsadar rayuwab ta kasa, talauci da kuma kudin shiga na daidaikun yan kasa da ita kasar kanta.

“Najeriya tafi dukkan kasashen Africa karfin tattalin arziki, amma tsadar reayuwar ta hauhawa take da kaso 18.5% , sai kasar South Africa da kaso 6.5% sannan sai Egypt da kaso 5%.

Amma talaucin Najeriya kaso 44.5 na yawan yan kasar, sai Egypt suna da kaso 32 .5% sai South Africa masu kaso 55.5% . A nan za’a ga duk Najeriya tafi yawan kason talauci, duk da tafi karfin tattalin arziki. Kenan zamu iya cewa abin da shugaban ya fada ba gaskiya bane”.

Buhari ne ya jawo muka fadi zaben gwamnan jihar Osun

Wani babban jigo a jam’iyyar APC a jihar Edo, John Mayaki, ya ɗora alhakin shan kashin da jam’iyyar tayi a zaɓen gwamnan jihar Osun akan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sanata Adeleke Ademola na jam’iyyar PDP ya dakatar da neman tazarcen gwamna mai ci Gboyega Oyetola.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe