
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi dakile kokari da burin abokin hamayyarsa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi.
Barin sa PDP babba kuskure ne
A cewar sa Mista Obi ya yi kuskuren ficewa daga jam’iyyar PDP kuma ba shi da tabbacin lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Atiku ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da Arise TV a ranar Juma’a.
Mista Obi, wanda shi ne mai rike da tutar jam’iyyar LP,wanda a da ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP kafin da ga baya ya fice daga jam’iyyar.
Ya bar PDP kwanaki kafin zabe
Ya bar jam’iyyar PDP kwana uku kafin zaben fidda gwani na shugaban kasa, tare da bayyana dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.
A zantawan da akayi da Atiku, ya yi watsi da dimbin magoya bayansa da tsohon gwamnan ya tara, inda ya ce an nemesu an rasa a lokacin zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala.
Ya kuma yi watsi da fargabar cewa ayyukan jam’iyyar LP za su yi illa ga kuri’un jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa.
“A gaskiya ba na tsammanin jam’iyyar Labour za ta amshe kuri’u da yawa daga PDP kamar yadda mutane ke zato. Ba su da tsari a kowane mataki, ba su da gwamna, da ’yan majalisa.
“Zai yi matukar wahala jam’iyyar Labour ta lashe zabe mai gabatowa.
“Sun ce a kafafen sadarwar zamani suna da kuri’u miliyan daya a jihar Osun amma kuri’u nawa suke da su a bayyane.
“A yankin Arewacin kasar nan, kashi 90 cikin 100 na mutane ba sa samun damar shiga kafafen sada zumunta. Yawancin masu zabe ba sa amfani da shafukan sada zumunta,” inji shi.
Atiku ya kuma ce Mista Obi “bai tuntube shi ba” kafin ya bar PDP.
” kwana uku bayan ya bar PDP sannan ya sanar da ni ya koma jam’iyyar Labour.”
ZABEN 2023: Muhimmin dalilin da zai sa dole na lashe zabe a shekarar 2023 – Inji Tunibu
Dan takarar jamiyya mai mulki ta APC, Bola Ahmad Tunibun, ya bayyana dalilin da zai sa dole ya lashe zabe shugaban kasa mai zuwa, na shekarar 2023.
Ga dalilin da zai sa ya lashe zaben
Kamar yadda yazo a rahoton Daily Post, tsohon gwamnan Legas din yace dole ne ya lashe zaben, saboda samar da aiki da yayi, ga matasa.
Tunibun yayi Wannan jawabin ne ranar Laraba, yayin da yake kaddamar da mataimakin sa Kashim Shettima, inda ya nanata da babban baki, cewa nasarar sa, zata kawar da duk wani raberaben addini da na kabilanci da suke damun ‘yan Najeriya.
Tunibun ya ja hankalin yan
Daga nan, sai ya ci gaba da jan hankalin yan Najeriya da su kara hada kan su, domin cigaban kasa, da kuma daukar kasar Najeriya a matsayin daya.
Abin jira a gani, shine lokacin zabe ko mafarkin Tunibu din zai zama gaskiya?
Allahu yaalamu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com