Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 50 a wani hari da suka kai a ƙauyen Kuchi cikin ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja.
A cewar wata sanarwa daga Yusuf Kokki, shugaban ƙungiyar ‘Concerned Shiroro Youths’ ta jihar Neja, ƴan bindigan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe biyu na daren ranar Asabar. Jaridar The Cable ta rahoto
Sun mamaye garin cikin tsakar dare
Kokki yace ƴan bindigan sun dira garin da yawan su lokacin da ake tafka ruwan sama, sannan sun yi ta bi gida-gida suna aikata ta’asar su.
Yace ƴan bindigan yanzu haka sun maƙale tare da mutanen da suka ɗauke a rafin Dangunu saboda cikowar da rafin yayi a dalilin ruwan sama.
Tabbatattun rahotanni da suke fitowa daga Kuchi, a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja, sun nuna cewa gungun ƴan bindiga sun farmaki ƙauyen cikin tsakar dare wanda a dalilin hakan suka yi awon gaba da mutane da dama. A cewar sanarwar.
Binciken da na gudanar ya ƙara bayyana cewa ƴan bindigan sun dira ƙauyen ne da misalin ƙarfe biyu na dare yayin da ake ruwan sama, inda nan take suka shiga gida-gida suna tattaro mutane domin tafiya da su maɓoƴar su.
Sai dai ya zuwa yanzu, ba rahoton wani wanda ya jikkata sai dai an yi ƙiyasin cewa an ɗauke mutum 50.
Ya roƙi gwamnati da ta tura jami’an tsaro
Ya roƙi gwamnati da ta tura jami’an tsaro zuwa ƙauyen domin dawo da kwanciyar hankali da cafke ɓata garin.
Ana buƙatar tura jami’ai da gagawa a halin yanzu domin tunkarar su a hanyar fitar su inda suke maƙale a yanzu. A tura ƴan sakai zuwa wurin. Yakamata hukumomin da abin ya shafa suyi gaggawar ɗaukar matakan da suka dace.
Sama da ƴan bindiga 100 ne suka halarci bikin nadin sarautar shugabansu da aka yi a jihar Zamfara
A wani labarin na daban kuma ƴan bindiga da dama sun halarci naɗin sarautar shugaban su a Zamfara.
Sama da ƴan bindiga 100, a ranar Asabar, suka halarci naɗin sarautar wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga mai suna Ada Aleru a matsayin Sarkin Fulani wacce sarkin Yandoto yayi masa.
Mutane a garin Tsafe jihar Zamfara sun ce ƴan bindigan sama da 100 sun halarci naɗin sarautar shugaban na su wacce sarkin Yandoto yayi masa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com