34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Kasar Saudiyya ta damke mutumin da ake zargi da taimakawa dan jaridar kasar Isra’ila shiga garin Makka

LabaraiKasar Saudiyya ta damke mutumin da ake zargi da taimakawa dan jaridar kasar Isra'ila shiga garin Makka
israel journalist mount arafat 760x485 1

An kama wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da dan jarida da ba musulmi ba cikin birnin Makkah mai tsarki, wanda hakan ya sabawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga garin.

Ya yi amfani da ziyarar shugaban kasar Amurka ya zagaye garin Makkah

Jami’an Saudiyya sun sanar a ranar Juma’a cewa dan jaridar kasar Isra’ila Gil Tamari, wanda ya je Saudiyya don bayar da rahotannin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai a can, ya yi amfani da damar don shiga masarautar, ya shiga cikin birnin Makkah, ya yi zagaya tare da watsawa gidan talabijin na Channel 13.

Sakin bidiyo ya haifar da cece-ku-ce

Watsa wannan bidiyo ya haifar da cece ku ce da kuma gargadin cewa zai iya lalata shirin da ake ganin ya wanzu tsakanin Saudiyya da Isra’ila.
Dan kasar ta Saudiyya shi ne ya taimakawa dan jaridar, wanda ke da izinin zama dan a kasar Amurka, zuwa babban birnin Makkah ta hanyar da aka kebance don musulmai kawai,wanda hakan ya sabawa ka’idoji.

Dole ne a kiyaye ka’idoji

Duk masu shigowa cikin masarautar dole ne su mutunta kuma su bi ka’idoji, musamman wadanda suka shafi wurare masu tsarki.
“Duk wani cin zarafi za mu dauke shi a matsayin laifin wanda baza a amince da shi ba,” in ji jami’in ‘yan sanda.
Jami’in ya ce an kuma yi karar dan jaridar “wanda ya aikata laifin” zuwa gaban kotu.
Makka garin Ka’aba, wuri mafi tsarki na Musulunci, wanda ke cikin Masallacin Harami.
Kakakin ya ce an ga Tamari a cikin wani bidiyo yana shawagi a kusa da babban masallacin Makkah tare da yin watsi da duk wata alama da ke kan titi da aka dan “wadanda ba musulmi ba.

Dan Jaridan kasar Isra’ila Ya Shiga kasar Makkah A asirce, Ya Hau Dutsen Arafah

Hotunan da wani dan jaridan kasar Isra’ila ya dauka ya yin shigar sa cikin birnin Makkah birnin da ya kasance mafi tsarki na Musulunci, bidiyon ya yi ta yawo a yanar gizo in da ya tayar da hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.

Ya,dauki kansa cikin jin dadi

Gil Tamari, editan labaran duniya a tashar Channel 13, ya yi rikodin kansa yana murmushi yayin da ya ziyarci birnin Makkah mai tsarki inda yake nuni da Masallacin Harami.An dai hangi Tamari a cikin motar sa ya na nuna masallacin Harami yana cewa burinsa na taka kafarsa a garin Makka ya cika.
Sakin hotunan sun yi matukar bada mamaki

Hotunan sun zo a bazata ga masu amfani da shafukan sada zumunta, duba da yadda a al’adance wanda ba musulmi ba zai shiga garuruwan Makkah da Madina ba, kamar yadda ayoyin kur’ani mai girma suka bayyana. An bayyana yadda Ba’isra’ilen ya samu damar shiga birnin mai tsarki; Masu amfani da shafukan sada sun bayyana cewa suna da yakinin ya shiga ne ba bisa ka’ida ba.

Ya yi rikodin kansa akan dutsen arfah

Dan jaridan ya yi rikodin din lokacin da ya hau Dutsen Arafat, inda Musulmai ke taruwa a lokacin aikin Hajji.
An hada faifan bidiyo mai cike da cece-kuce ta Channel 13 da taken “Gil Tamari dan jaridar Isra’ila na farko da ya shigo ya fita.
Wannan lamari ya sabawa dokar da aka kafa ɗaruruwan shekaru a cikin birni mai tsarki kuma masu amfani da kafofin watsa labarun sun soki wannan lamari a matsayin rashin mutunta al’adu da ayyukan Musulunci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe