34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Saura Kiris na mutu – Inji dan dambe Mike Tyson

LabaraiSaura Kiris na mutu - Inji dan dambe Mike Tyson

Sananen dan damben duniya, Mike Tyson ya bayyana cewa, saura kiris mutuwa ta riskeshi. 

Da yake magana a wani shirin rediyo mai suna ‘Hotboxin tare da Mike Tyson’ ya bayyana yadda yake fama da rigingimun kudi, duk da kasancewar sa mamallakin makudan miliyoyi. 

Dalilin dan dambe Tyson din na tunanin mutuwa a kusa

Yace yana ji a jikin sa, mutuwar sa daf take da riskar sa. Inda ya kara da cewa,

dan dambe
Saura Kiris na mutu – Inji dan dambe Mike Tyson

 

” Dukkanin mu zamu mutu tabbas wata rana. Idan na kalli madubi, sai naga wadannan yan kananan dugo-dugo a fuskanta, sai nace to fan ! Wannan yana nufin lokacin tafiya ta ya kusa, tabbas ya kusa.”

 

” Ni kudi ba shine komai a gareni ba, na sha fadawa mutane. Suna tunanin kudi zai saka su dukkanin farin ciki, hum! dan basu taba samun makudan kudade bane, saboda idan ka sami kudi makudai, babu wanda zai soka soyayyar gaskiya. Yaya za’a yi na gane soyayyar gaskiya, idan mutum yana da dala biliyan dari biyar $500b a a cikin asusun sa na banki?

Da fitacciyar sana’ar sa ta dambe, Tyson din shine matashi na farko, dan shekara 20 da ya fara gasar jibga-jibgan mutane, a dambe. Inda yake shiga gasar masu nauyin kilo 50 zuwa 60 a lokacin sa.

Dan Wasan Dambe Mike Tyson ya yi alkawarin ba da Kyauta mai tsoka Ga Duk Wanda ya amince da auren Diyar sa

Shararren dan wasan dambe na kasar Amurka, Michael Gerard Tyson ya shelanta ba da kyautar zunzurutun kudade dala na gugan dala har Dalar Amurka milyan 10 ga duk mutumin da ya amince ya yarda zai yi wuff da diyarsa.

Diyar ta sa mai suna Mitchell Tyson wacce ta kasance tana da shekaru 32 a duniya.
Sai muce Allah ya bawa mai rabo sa’a

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe