23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An cafke wani matashi yana yiwa wata mahaukaciya fyade a Neja

LabaraiAn cafke wani matashi yana yiwa wata mahaukaciya fyade a Neja

Ƴan sanda sun cafke wani matashi mai suna Haruna Musa, mai shekara 21 a duniya, wanda aka kama dumu-dumu yana yin fyade ga wata mahaukaciya a Angwan Gwari Kwamba cikin ƙaramar hukumar Suleja, ta jihat Neja a daren ranar Talata.

A wani bidiyo da jaridar Daily Trust ta samo, an jiyo Musa yana cewa bai riga da ya shiga matar ba kafin ta fara ihu wanda ya fargar da mutane. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Matashin ya bayyana abinda yaja hankalin sa wurin ƙoƙarin yiwa mahaukaciyar fyade

Musa, wanda aka same shi ƙullin tabar wiwi, ya ɗora alhakin abinda ya aikata akan shaye-shaye da kuma tsinuwa daga ƙauyen shi. Ya ƙara da cewa halin tsirarar da matar take ciki shine abinda ya ja hankalin shi zuwa gare ta.

Ya bayyana cewa:

Idan da ba don jami’an tsaro ba da ƙila sai na sadu da ita. Ban san abinda ya shige ni ba. Ku yafe min. Shekara ta 21 kawai a duniya. Ina da abubuwa da dama a zuciyata. Matsalolina sun fi ni ƙarfi. Bani da kowa wanda zai taimaka min.

A Najeriya matsalar fyade na daɗa ƙaruwa musamman akan ƙananan yara maza da mata. Yara da yawa na fuskantar matsalar fyade idan sun fito daga gidajen iyayen su.

Ba ƙananan yara kaɗai ba, har ƴanmata da matan aure ba su tsira ba daga wannan babbar matsalar da ake fama da ita a ƙasar.

Yan sanda sun cafke wani matashi bisa laifin yiwa tsohuwa ‘yar shekara 75 fyade

A wani labarin na daban kuma ƴan sanda sun yi ram da wani matashi bisa laifin yiwa wata tsohuwa ƴar shekara 75 fyade.

Yan sanda a jihar Anambra a ranar Asabar sun cafke wani mutum mai shekara 30 a duniya bisa zargin yin fyade ga wata tsohuwa mai shekaru 75 a duniya.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar a birnin Awka.

Yace wanda ake zargin, wanda ɗan asalin ƙauyen Eyiba ne a jihar Ebonyi, an cafke shine da misalin ƙarfe 4 na yamma ranar Juma’a a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe