24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ban taba sanin ina da ciki ba, Budurwar da ta haihu daga shiga bandaki

LabaraiBan taba sanin ina da ciki ba, Budurwar da ta haihu daga shiga bandaki

Wata mata mai shekaru 22 ta sha mafi girman mamaki a rayuwarta bayan ta haifi jaririya daga shiga bandaki, Legit.ng ta ruwaito.

Bata dade da yin al’adarta ta watan ba

Lucy Jones, wata mata da ke zama a Bristol da ke Ingila, ta ce bata san tana da juna biyu ba kasancewar bata dade din yin al’adarta ta duk wata ba.

Kamar yadda New York Post ta ruwaito, matar ta sha mamaki bayan ta je bandaki inda taji wasy alamu na nakuda, sai hango kafafu tayi suna fitowa daga jikinta.

Ta yi gaggawar kiran ma’aikatan lafiya na gaggawa wadanda su ma sun sha mamaki bayan ganin lamarin.

A cewarta:

“Ban san ina da juna biyu ba sai da na shiga bandaki naga jariri na fitowa.”

Lucy, wacce ma’aikaciyar jirgin sama ce ta bayyana yadda ta dinga fama da ciwon baya da na ciki ana gobe lamarin zai auku.

Ta ce ta dade tana shan maganin hana haihuwa, ashe duk bai yi aiki ba.

Matashi ya wallafa hoton bandakin wani Otal da ya sauka a Ibadan, ya ba kowa mamaki

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya wallafa hoto inda ya ce na wani otal ne a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda hoton ya nuna, tukunya ce ta dalma aka sagala a jikin bandakin wacce za ta dinga tara ruwa.

Lamarin ya ba kowa mamaki inda ake ta cewa wannan wanne irin otal ne mara tsari.

zanotti_blaze ya ce:

“Masu kula da otal dinnan ba za su mutu cikin salama ba, menene kuma wannan?.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe