Wani malamin jami’a ya umarci dalibinsa ya kwashi rawa akan maki 10, shafin Instablog9ja na Facebook ta ruwaito.
Kamar yadda bidiyon ya nuna, an ga dalibin a gaban aji yana kwasar rawa yayin da sauran dalibai su ke ihu suna kara masa kaimi.
Kamar yadda aka gani a bidiyon, malamin na tsaye a gefe ba tare da ya sa sauti ba, dalibin ya dinga kwasar rawa yana kurda kafafunsa.
Anga yadda malamin yake gyada kai da alamu rawan ya yi matukar burge shi kuma da wuya idan ba zai ba shi cikakken maki ba.
Yadda mazaunan roban da wata budurwa tayi ciko dasu su ka zame tana tsaka da rawa
Wata budurwa ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani bayan ta sanya mazaunan roba amma kuma su ka zame tana tsaka da rawa a wani fati, Adomo online ta ruwaito.
Budurwar ta je wata liyafa ne kuma ta sanya wata riga gajera mai kalar koriya da kuma farin takalmi rufaffe.
Tana tsaka da kwasar rawa tare da wani mutum kamar yadda sauran ‘yan matan da su ka je su ke kwasar rawa yayin da wasu kuma su ka tsaya a gefe su na ba idanunsu abinci.
Duk da yadda ta dauki wankan amma kuma abu guda ne ya gama kwafsata.
Yanayin yadda mazaunanta su ka zauna sun bai wa kowa mamaki don daga gani na roba ta sanya su ka zamiye saboda tsabar rawan da ta sha.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com