Sojojin Najeriya sun tabbatarda cewa, an kara kubutar da wata yar Chibok mai suna Ruth Bitrus, ita da danta, daga hannun yan ta’addan Boko Haram.
Kwamanda yayi jawabi ga sojojin Najeriya
Kwamandan atisayen Hadin Kai, mai suna Manjo janar GC Musa, shine ya fadi hakan Jiya a Maiduguri, yayin da yake mika kayan tallafin kiwon lafiya da hukumar cigaban yankin Arewa maso gabar ta baiwa asibitoci 7 na gundumomin rundunar.
” Idan zaku iya tunawa, yan satittika da suka wuce, mun kubutar da yan matan Chibok guda biyu, tare da yaran su, Ina so in shaida muku cewa, mun sake ceto wata ma, ta ukun kuma yanzu ita ce muke kokarin cetowa.
Kwamandan ya fada.

Sojoji zasu dage suyi duk mai yiwuwa domin kubutar da yan matan
Manjo janar Musa din, ya kara da cewa sojojin zasu ci gaba da ceto ‘yan matan, wadanda a cikin su har da Leah Sharibu, wadda har yanzu tana hannun yan ta’addan Boko Haram din.
” Ba zamu huta akan hakarkarin mu ba, har sai mun tabbatarda Leah Sharibu, da sauran yan matan Chibok sun dawo, baza mu huta ba, har sai mun tabbatar da sun dawo gida lafiya. Manjo janar Musa din ya fada
Manjo janar Musa din ya fada
Idan za’a iya tunawa, yan satittika da suka gabata, rundunar sojojin sun kubutar da yan mata biyu
Mary Dauda da kuma Hauwa Joseph da ‘ya’yan su.
Mayakan ISWAP sun kashe mutane 25 bayan sun farma kauyuka 4 a jihar Borno
A kalla mayakan gungiyar ISWAP sun kashe mutane 25 a wadansu hare-hare mabanbanta da suka kai a kudancin jihar Barno.
An gano cewa kungiyar ISWAP sun yi wa kauyen Sabon-gari na karamar hukumar Damboa, a ranar Asabar ,inda suka hallaka a kalla mutane 11.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: