24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

ZABEN 2023: Muhimmin dalilin da zai sa dole na lashe zabe a shekarar 2023 – Inji Tunibu 

LabaraiZABEN 2023: Muhimmin dalilin da zai sa dole na lashe zabe a shekarar 2023 - Inji Tunibu 

Dan takarar jamiyya mai mulki ta APC, Bola Ahmad Tunibun, ya bayyana dalilin da zai sa dole ya lashe zabe shugaban kasa mai zuwa, na shekarar 2023. 

Ga dalilin da zai sa ya lashe zaben

Kamar yadda yazo a rahoton Daily Post, tsohon gwamnan Legas din yace dole ne ya lashe zaben, saboda samar da aiki da yayi, ga matasa. 

dalilin da zai sa
Muhimmin dalilin da zai sa dole na lashe zabe a shekarar 2023 – Inji Tunibu

Tunibun yayi Wannan jawabin ne ranar Laraba, yayin da yake kaddamar da mataimakin sa Kashim Shettima, inda ya nanata da babban baki, cewa nasarar sa, zata kawar da duk wani raberaben addini da na kabilanci da suke damun ‘yan Najeriya. 

Tunibun ya ja hankalin yan

Daga nan, sai ya ci gaba da jan hankalin yan Najeriya da su kara hada kan su, domin cigaban kasa, da kuma daukar kasar Najeriya a matsayin daya.

Abin jira a gani, shine lokacin zabe ko mafarkin Tunibu din zai zama gaskiya? 

Allahu yaalamu.

Dalilan da su ka sanya Ganduje yafi cancanta da zama mataimakin Tinubu a APC -Hadimin gwamna

A yayin da ake tsaka da neman shawarwari kan wanda zai zama mataimakin shigaban ƙasa ga ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wani mai taimakawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan harkokin sadarwa, Shehu Isa, ya kawo dalilan da su ka sanya Ganduje yafi dacewa APC da Tinubu su ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Isa wanda yayi ƙarin haske kan takarar musulmi da musulmi, inda yake cewa ba sji a cikin kundin tsarin mulki, yayi nuni da cewa Ganduje shine yafi cancanta da zama mataimakin Tinubu a ƙarƙashin jam’iyyar. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

 

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe