31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Rumbun ma’ajiyar wutar lantarki na kasa ya sake durkushewa kwanaki 20 kacal da gyara shi

LabaraiRumbun ma'ajiyar wutar lantarki na kasa ya sake durkushewa kwanaki 20 kacal da gyara shi

Rumbun ma’ajiyar wutar lantarki na kasa, ya sake lalacewa, inda ya koma babu makamashin wuta ko daya a cikin sa, abin da ya kara tsunduma kasar a cikin bakin duhu.

Hakan yana zuwa ne, kwaki 38 bayan gyara irin makamanciyar matsalar a 12 ga watan Yuli da ya gabata, kwana 20 kenan bayan hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta yi wata kwarya-kwaryar, kwangila da masu hadahadar kasuwancin wutar, domin samar da akalla wutar mai karfin mega wat 5,000MW ko kuma a kalla 4,000MW.

wutar lantarki
Rumbun ma’ajiyar wutar lantarki na kasa ya sake durkushewa kwanaki 20 kacal da gyara shi

Rumbun ma’ajiya wutar lantarkin ya tashi fanko

Wannan durkushewa da Rumbun ma’ajiyar wutar lantarki na kasa yayi, wanda shine na biyar a wannan shekarar, ya faru ne da misalin karfe 12 na rana, inda kawai Rumbun ya tashi babu komai a cikin sa. 

Da misalin karfe 11 na safe, bayanai daga bangaren yada bayanai na Najeriya, sun nuna cewa, karfin wutar da take cikin Rumbun ta ragu da kasa da 3,000MW da kuma da 2,000MW ta ragu, duk da cewa tana samun karfin lantarki daga camfanoni goma sha tara, 19 na (GenCos).

Ta inda wutar lantarkin take samuwa

Kaso mai yawa na wutar, yana zuwa ne daga kamfanin Delta Gas, wadda yake samar da mega wat, 453MW da kuma kamfanin Azura shi kuma yana samar da mega wat 448MW, inda shi kuma na Dadin Kowa ya koma fanko, babu komai na makamashin wuta a cikin sa.

Tun farko,  hukumar yada bayanai, da kuma  manajan kula da Rumbun ma’ajiyar wutar, basu fadi musabbabin durkushewar Rumbun wutar lantarkin ba.

An gama daukan duk matakan kawo karshen matsalar wutar lantarkin Najeriya – Minista

Bayan taron gaggawar da ministan wutar lantarki ya kira, Engr. Abubakar Aliyu, a ranar 14 ga Maris, 2022, don dawo da samar da wutar lantarki na ƙasa baki daya da kuma samar da wani tsari mai dorewa na inganta samar da wutar lantarki, ma’aikatar ta fitar da wata sanarwa don faɗakar da masu amfani da bayanai kan ci gaban da aka samu kawo yanzu don magance matsalar kwanan nan, The Leadership ta ruwaito.

Engr. Aliyu a cikin waya sanarwar, ya tunatar da cewa, wutar lantarki ta ƙasa ta yi asarar kusan ƙarfin samar da megawatt 1,100 sakamakon katsewar iskar gas da ake samu a tashoshin wutar lantarki na Okpai, Calabar da Afam VI a lokaci guda.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe