34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Hukumar JAMB ta bayyana maki 140 a matsayin mafi karancin maki

IlimiHukumar JAMB ta bayyana maki 140 a matsayin mafi karancin maki
JAMB UTME

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta amince da 140 a matsayin mafi karancin makin da ta yankewa jami’o’i a shekarar 2022.

Politeknic da kwalejojin ilmi suma an kayyade nasu

Mafi qarancin makin da aka yanke wa makarantun politeknic shine 100 yayin da kwalejojin ilimi suma100.
An bayyana hakan ne a taron tsarawa da ake yi kan shiga makarantun gaba da sakandare wanda ministan ilimi Adamu Adamu ya jagoranta a Abuja ranar Alhamis.
Magatakardar Hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede a baya ya nuna mafi karancin maki da manyan jami’o’i suka dauka.
Ba kamar shekarar 2021 ba, duka jami’o’i zasuyi amfani da maki iri daya a shekarar 2022.

Kason cancanta ga kowace jami’a zai kasace kashi 45

A cewarsa, ga jami’o’in tarayya, kason cancanta zai kasance kashi 45 cikin 100 yayin da na jami’o’in jihar ya fada tsakanin kason ‘yan asalin jihar da kason sauran ‘yan kasa.
“Mafi chanchatar kason maki a kowace Jiha shine kashi 10 na farko ba tare da la’akari da ina dalibi ya fit ba, kashi 35 cikin 100 shine aka amince wa ‘yan asalin jihar,” in ji shi.
Kimanin dalibai 1,761,262 ne suka nemi shiga jami’o’in a 2022 Unified Tertiary Matriculation Board UTME, yayin da 98,270 suka nemi shiga jami’o’in kai tsaye (DE).
Taron, ya cimma matsaya cewa ranar 31 ga watan Disamba zai kasance ranar ƙarshe na,bada gurbin karatu a duk jam’i’o’i gwamnati da masu zaman kansu a duk faɗin ƙasar.
A halin da ake ciki, ministan ilimi ya shawarci makarantun gaba da sakandare da su dauki matsayi mai sauki a cikin tsarin shiga jami’o’in idan har duk wasu abunda ake nema sun yi daidai da ƙa’idodin.

Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan

Mai martaba tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido, tare da mai martaba sarkin Zazzau ambasada Nuhu Bamalli, sun halarci bikin kammala karatun dan tsohon sarki Sunusin, mai suna Mustapha Lamido Sanusi.

Sakamakon da dan sarki Sunusi Lamidon ya samu
An tattara rahoton cewa, Mustapha din ya fita da sakamako ajin farko, wato (first class ) a fannin ilimin tattalin arziki, a wata jami’a Portsmouth dake birnin Landan.

A lokacin bikin, sarkin yayi kira ga yaron da ya kammala digirin, da yayi amfani da ilimin nasa wajen samar da cigaba da tallafawa marasa karfi.

Dalilin neman ilimi , inji sarki Sunusi
A fadar sa, yace babban dalilin da yasa ake yin ilimi shine domin a kyautata gobe, da kuma yin hidima ga al’umma.

Da take nagana a yau, sarkin ya ce, Mustapha din ya yi nuna hazaka da ta daga darajar Najeriya, inda ya kara da cewa, dukkanin dalibai da suke karatu a kasashen waje, suyi Koyi da shi domin su fita da kyakkyawan sakamako.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe