27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar dakatar da acaɓa a kwata-kwata a Najeriya

LabaraiGwamnatin tarayya na duba yiwuwar dakatar da acaɓa a kwata-kwata a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar hana sana’ar acaba kwata-kwata a duk faɗin Najeriya.

Ministan Shari’a kuma antoni janar na ƙasa, Abubakar Malami ne ya sanar da haka ranar Alhamis, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Bincike ya nuna yadda ƴan ta’adda ke samun kuɗaɗen shiga

Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa ana amfani da ƴan acaɓa wurin haƙar ma’adanai a ƙasar nan sannan hana acanar zai taimaka wurin daƙile hanyoyin samun kuɗin shigar ƴan ta’adda da ƴan bindiga.

Ministan wanda yake tare da ministocin harkokin cikin gida dana harkokin ƴan sanda, Rauf Aregbesola da Mohammed Dingyadi, yace taron ya mayar da hankali ne kan hanyoyin da ƴan ta’addan ke amfani da su domin a dakatar da ayyukan su.

Ƴan ta’adda sun sauya salo

Yace gwamnati na buƙatar ta ɗauki mataki saboda ƴan ta’adda sun sauya daga tsoffin hanyoyin samar da kuɗaɗen su zuwa haƙar ma’adanai da amsar kuɗaɗen fansa.

Malami yace ƴan bindigan na amfani da babura wurin tafiye-tafiye, yayin da haƙar ma’adanai ke samar musu da kuɗaɗen siyen makamai.

Dangane da ko gwamnati zata duba abinda hana acaɓar da haƙar ma’adanan zai jawo ga talakawan Najeriya da kuma tattalin arziƙi, sai ministan ya kada baki yace gwamnatin tarayya zata fifita buƙatar ƙasa fiye da ta wasu tsirarun mutane.

Da yake na shi jawabin, ministan harkokin cikin gida, Aregbesola, ya an yi ƙoƙari sosai wajen tattara bayanan sirri kafin kai harin da aka kai gidan yarin Kuje, amma ya koka kan yadda aka kasa yin abin da ya dace a kai.

Ya kuma ce tuni aka miƙa wa shugaba Buhari sakamakon binciken na farko-farko, inda ya bayar da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a fitar da cikakken sakamakon da zarar an kammala bincike.

Aregbesola ya ce duk wadanda aka gano sun yi sakaci da aikin su, za su fuskanci hukunci.

Gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin kammala aikin titin Kaduna-Zaria-Kano

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin gama aikin titin hamyar Kaduna-Zaria-Kano

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa aikin hanyar Kaduna-Zaria zuwa Kano, sashin biyu na hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano zai kammalu kafin ƙarshen wannan shekarar.

Da yake magana yayin duba yadda aikin ginawa da gyaran hanyoyin yankin jihohin arewa maso yamma, darektan ginawa da gyaran manyan tituna a ministirin aiki da gidaje, Engr. Folurunso Esan, yace aikin sashi biyu na hanyar na tafiya yadda aka tsara

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe