Wata budurwa ta auri mahaifin saurayin ta mai shekaru 89 a duniya bayan ta kama saurayin nata yana cin amanar ta.
Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa an saka hoton budurwar mai shekaru 23 a kafar sadarwa ta Instagram. Shafin The Savoy Show shine ya saka hotunan yarinyar a kafar ta Instagram.
Budurwar tayi martani mai zafi ga masu tsokanar ta
Da take mayar martani ga masu tsokanar ta kan abinda ta aikata, budurwar ta soke mutane masu kiranta da mutumiyar banza.
A wani faifan bidiyo da shafin ya saka, budurwar tayi magana kan yadda saurayinta wanda yanzu sun rabu, yaci amanarta tare da mata daban-daban ciki kuwa har da ƙawayen ta.
Kaɗan daga cikin abinda budurwar tace shine:
Yanzu ana kirana da mutumiyar banza saboda na auri mahaifin tsohon saurayina, amma shi tsohon saurayin nawa wanda yaci amanata da mata da yawa ciki har da ƙawayena, ba’a kira shi mutumin banza ba.
Mutumin da yana can yana yamaɗiɗin sa. Amma aa ni ce mutumiyar banza.
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
jay_west.42 ya rubuta cewa:
Kawai don yayi abinda yayi bai nufin abinda ki kayi daidai ne. Meyasa mata ke ƙoƙarin gasgata ɗabi’un su ta hanyar haɗa kan su da mazan da suke cewa sun fi su?
lashaunhaywood ya rubuta cewa:
Shekarun sa 89 tare da dukiyar dala miliyan 90, ina tunanin hakan ya sanya kikai wuff da shi, amma ku sani bana jin haushin ta
Lamba ta maza ke amsa maimakon siyan kayan sana’a ta, Dirarriyar budurwa ta koka
A wani labarin kuma wata dirarriyar budurwa ta koka kan yadda samari ke rubububin amsar lambarta maimakon siyan kayan tallar ta.
Wata dirarriyar budurwa wacce ke sana’arta ce siyar da ruwan leda da na gora tare da lemuka ta koka akan yadda hankalin samari ya fi karkata akanta maimakon kayan sana’arta, Amihad.com ta ruwaito.
Tana sana’ar ne birnin Accra da ke kasar Ghana don ta rufawa kanta asiri, amma abinda ya fi ci mata tuwo a kwarya shi ne yadda aka fi neman lambar wayarta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com