27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Yadda budurwar miji ta kai kararsa wurin matarsa bayan ya yi mata karyar matarsa ta rasu

LabaraiYadda budurwar miji ta kai kararsa wurin matarsa bayan ya yi mata karyar matarsa ta rasu

Dani Bose, wata kyakkyawar baturiya ta fallasa wani mutum ga matarsa wacce yayi shekaru 30 da aure bayan ya ha’inci matar, Legit.ng ta ruwaito.

Ya ce matarsa ta mutu, ashe karya yake

‘Yar TikTok din mai shekaru 21 ta bayyana cewa mutumin ya yi mata karyar cewa matarsa ta mutu kuma yana ta fatan samun wani lokaci don su yi nishadi tare.

A bidiyoyin nata, ta bayyana cewa matarsa ce ta tuntube ta don ta taya ta bincike idan har mijinta na shekaru 30 yana cin amanarta.

Kamar yadda ta wallafa:

“Barka, diyata ta nuna min bidiyoyin ki masu kayatarwa na kafafen sada zumunta. Zan so sanin farashin da zaki amsa don ki bincika min mijina, ko taimaka min.”

Kamar yadda New York Post ta ruwaito, mutumin ya tura sako ga Bose yayin da yake neman kulla alaka da ita, sannan ya rage shekarunsa inda yace mata matarsa ta mutu.

‘Yan mata da matan aure su na bada lambar mazajensu don ta gwada su

‘Yan mata da matan aure masu zargin samarinsu da mazajensu su na biyan kyakkyawar budurwar ne don ta bincika musu gaskiyar halayensu.

Dani ta amince da bukatar wata mata wacce mijinta ya tura mata sako ta WhatsApp. Daga nan Dani ta tura wa matarsa sakon mai ban tsoro.

Kano: Daga zuwa siyo mata Shawarma, budurwa ta tsere da motar saurayinta

Jami’an ‘yan sanda sun yi ram da wata budurwa bayan ta tsere da motar saurayinta wanda ya fito siyo mata Shawarma a Unguwar Kofar Famfo da ke Birnin Kano, Aminiya ta ruwaito.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai yadda komai ya wakana.

A bangaren Ilham kuwa ta ce wani saurayinta ta kira don ya tuka mata motar gida don ya ajiye mata motar a gidansu har sai ta amshi kudinta a hannun saurayin.

An kama saurayin nata wanda ya taya ta satar motar don ci gaba da bincike.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe