31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Rashin iyayen gida da kudi ke hana ‘yan fim tasiri a siyasa, Jarumi Hamisu Iyantama

LabaraiKannywoodRashin iyayen gida da kudi ke hana ‘yan fim tasiri a siyasa, Jarumi Hamisu Iyantama

Tsohon jarumin Kannywood wanda ya shahara a baya, Hamisu Iyantama, a wata murya da shafin DW Hausa tayi na hira da shi, ya warware zare da abawa dangane da abubuwan da ke kawo nakasu ga siyasar ‘yan fim.

Kamar yadda yace, rashin iyayen gida da kudi, su ne abubuwan da ke kawo cikas yake sanyawa ko da ‘yan fim sun fito takara, duk da saninsu da aka yi, sai kaga ba sa tasiri.

Yayin da aka tambayeshi abinda ya ke sanyawa jaruman fina-finai su kasa cimma gaci a siyasance, ya fara da cewa:

“Waye ya tsaya maka? Kana da kudi ko baka da kudi? Wannan abubuwan guda biyu su suke sanyawa ake samun nasara kusan kaso 75 a siyasar Najeriya.

“Idan kana da ubangidan da ya daure maka gindi, ko ba kada da kudi, to shikenan a siyasa za a tsayar da kai, za a tallafa maka har a nemo kudin, ace ka tsaya kuma a baka jama’a, ko ka san su ko baka san su ba, ace su zabe ka.

“An sha dauko mutanen da ba a san su ba, su ba kowa bane, dan fim ya fi su daraja a idon mutane, an fi sanin dan fin fiye dasu, amma saboda ‘yan fim ba su da ubangida, wancan da aka kawo yanzunnan za a tallata shi kuma ya karbu saboda wancan ubangidan nashi ya isa ya juya siyasar da ake ciki.”

An tambaye shi dalilin da ya hana shi tasiri a siyasance a takarar da ya tsaya a baya, inda yace ba su kafu ba a kananun hukumomi 42 da ke cikin Kano.

Ya kara da cewa ba su da isasshen kudin da ake bukata wurin kafa jam’iyya saboda a sabuwar jam’iyya su ka je ma siyasar Kano sannan babu wasu manyan mutane da suka karbi jam’iyyar tasu.

Ya kara da cewa siyasa tana da bambanci da soyayyar da ake yi wa ‘yan fim. Kuma tasirin yana zuwa ne da jam’iyyar da mutum ya tsaya.

Dan wasa kwallon kafa Ahmed Musa ya yi wa ‘yan siyasa raddi game da yadda suka yi biris da yajin aiki da malaman jami’o’i ke yi

Har yanzu babu wani yunkurin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara ba, kyaftin din kungiyar Super Eagles, Ahmad Musa ya diga ayar tambaya kan ingancin wadanda nauyin ya rataya a kansu domin nemo hanyar magance matsalar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Musa ya bayyana cewa masu mulkin kasar nan ba su yarda da tsarin da suke gindaya ba, shi ya sa suke tura ‘ya’yansu kasashen waje karatu yayin da ‘yan kuci ku bamun kasar ke ci gaba da zaman gida .
In ba a manta ba Kwanan nan ne aka cika yanar gizo da hotunan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yayin da ya halarci bikin yaye dansa a jami’ar U.K.

Kungiyar kare hakkin musulmai ta Bukaci da a dage Jarabawar NECO da za a yi Ranar Sallah

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO da ta sauya ranar jarrabawar da za a yi a ranar Asabar 9 ga watan Yuli shekarar, 2022, sakamakon ranar ta fado ranar farkon sallah
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan roko ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata sanarwa.

Shugaban kungiyar ya yi jawabi

“Hukumar NECO ta sanya daya daga cikin jarrabawar ta mai suna Data Processing (Practical) a ranar Asabar 9 ga watan Yuli daga karfe 10.00 na safe zuwa 1.00 na rana,wanda wannan ranar ta ci karo da ranar farko ta ranar Sallah.
“Duba jadawalin jarabawar NECO 2022 (2022 NECO June/July SSCE Time-Table Examination Time-Table (27th June – 12th August, 2022) | Original Version.Muna da cikakkiyar masaniyar cewa ba da gangan aka saka wannan ranar ba domin a zahiri NECO ta bada hadin kanta ta hanyar bada hutu na tsawon mako guda don bikin Sallah (Litinin, 11 ga Yuli zuwa Juma’a 15 ga Yuli) kuma hakan ya bayyana a cikin jadawalin,” in ji Akintola.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe