A wata tattaunawa da BBC Hausa a shirin Daga Bakin Mai Ita da suka yi a ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, Jaruma Hauwa Waraka ta bayar da takaitaccen tarihinta.
Da farko ta fara da bayyana cewa sunanta Hauwa Abubakar amma an fi saninta da Hauwa Waraka, an haifeta a garin Jos amma a garin Kano ta girma.
Da aka tambayeta yadda aka yi ta shiga fim, ta ce da farko bata san menene fim ba ma. Akwai wasu ‘yan uwanta ne da suka kai ta Sabon Titi da ke Kano inda asalin ‘yan fim suke, daga nan ta dan fara shiga harkar jefi-jefi.
An tambayeta da fim din da ta fara, inda tace ta fara da kananu ne wadanda ba ita bace jarumar da ta haska fim din, don ko shirin Waraka wanda tayi fice dashi ba ita bace babbar jaruma a fim din.
Ta ce bayan ta dan yi fina-finai ta bar industiri na kusan shekaru 5 zuwa 7 wanda daga bisani ta dawo. Dama kuma tunda asali bata san menene fim ba dama kawai tana yi ne sama-sama.
Da aka tambayeta dalilin da yasa take fitowa a mutimiyar banza, sai tace ta san babu kyau a musulunce ayi shaye-shaye, da sauransu, amma kawai suna yi ne don fadakarwa kuma ita har yau bata shaye-shaye.
Ta ce bata jin dadin kallon da mutane suke yi mata, amma kuma tunda babu mai wuta ko Aljanna, ko kadan bata damuwa.
Ta ci gaba da cewa:
“Na yarda da Allah, na yarda da mazonnin Allah, na yarda da sunnoninsa, na yarda da mala’ikunsa, na yarda da littafansa, kuma na yarda da ranar kiyama, kuma na yarda da kalmar La’ilaha illallahu Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam.
“Kuma ni abinda nake gaya wa al’umma na san mutum dai bai da makullin wuta bai da makullin Aljanna. Balle yace ai nine mai makkulin wuta, wuta zan kai ka ko kuma nine mai makullin Aljanna, Aljanna zan kai ka.
“Don majority mutane kallon da su ke mana, inda su suke bada Aljanna, majority mutane ba za su ba dan fim ba. Magana ta gaskiya, saboda akwai mutanen da ko sunana aka kira, sai kaji sun ce wannan makamashin wutar? Ni kuma naga baka da wuta baka da Aljanna. Allah shi ke bada ita ba mutum ba.”
An titsiye faston da ke karbar N310,000 wurin mabiyansa don ya kai su Aljanna a gaban kotu
Wata kotun majistare ta Jihar Ekiti da ke cikin Ado-Ekiti ta bada belin fasto Noah Abraham Adelegan na cocin Christ High Commission na Omuo Oke-Ekiti, Daily Trust ta ruwaito.
Fasto Abraham shi ne wanda ya ce wa mambobin cocinsa zai iya kaisu aljanna, tare da cewa Omuo-Ekiti shi ne kofar shiga aljannar kuma zai fara tsagewa, sannan ya bukaci mambobin cocin da su biya N310,000 kafin su samu damar shiga aljanna.
Takardar gurfanar da faston ta zo kamar haka:
“An gurfanar da kai, Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afirilu, a Omuo Oke-Ekiti a cikin alkaryar Magistare, bayan ka yi ikirarin bogi, da burin damfara, ka gabatar da kanka a taron jama’a a cocin Christ High Commission, Omuo, Oke-Ekiti da cewa kana da damar kaisu aljanna kafin tsagewar kofar tare da cewa su biya kudi daga N300,000 zuwa N310,000 ko wannensu.”
Wanda ya gurfanar, sifeta Johnson Okunade, ya ce laifin ya ci karo da sashi na 416 na jerin kundin laifukan Jihar Ekiti na shekarar 2012.
Mai kare wanda ake tuhuma, Adunni Olanipekun, ya bukaci kotu ta bayar da belin wanda yake karewa, tare da cewa ya shirya gabatar da tsayayyu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com