34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Dan Jaridan kasar Isra’ila Ya Shiga kasar Makkah A asirce, Ya Hau Dutsen Arafah

LabaraiDan Jaridan kasar Isra'ila Ya Shiga kasar Makkah A asirce, Ya Hau Dutsen Arafah
israel journalist mount arafat 760x485 1

Hotunan da wani dan jaridan kasar Isra’ila ya dauka ya yin shigar sa cikin birnin Makkah birnin da ya kasance mafi tsarki na Musulunci, bidiyon ya yi ta yawo a yanar gizo in da ya tayar da hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.

Ya,dauki kansa cikin jin dadi

Gil Tamari, editan labaran duniya a tashar Channel 13, ya yi rikodin kansa yana murmushi yayin da ya ziyarci birnin Makkah mai tsarki inda yake nuni da Masallacin Harami.An dai hangi Tamari a cikin motar sa ya na nuna masallacin Harami yana cewa burinsa na taka kafarsa a garin Makka ya cika.

Sakin hotunan sun yi matukar bada mamaki

Hotunan sun zo a bazata ga masu amfani da shafukan sada zumunta, duba da yadda a al’adance wanda ba musulmi ba zai shiga garuruwan Makkah da Madina ba, kamar yadda ayoyin kur’ani mai girma suka bayyana. An bayyana yadda Ba’isra’ilen ya samu damar shiga birnin mai tsarki; Masu amfani da shafukan sada sun bayyana cewa suna da yakinin ya shiga ne ba bisa ka’ida ba.

Ya yi rikodin kansa akan dutsen arfah

Dan jaridan ya yi rikodin din lokacin da ya hau Dutsen Arafat, inda Musulmai ke taruwa a lokacin aikin Hajji.
An hada faifan bidiyo mai cike da cece-kuce ta Channel 13 da taken “Gil Tamari dan jaridar Isra’ila na farko da ya shigo ya fita.
Wannan lamari ya sabawa dokar da aka kafa ɗaruruwan shekaru a cikin birni mai tsarki kuma masu amfani da kafofin watsa labarun sun soki wannan lamari a matsayin rashin mutunta al’adu da ayyukan Musulunci.

Saudiyya ta bawa jiragen kasar Isra’ila damar shiga kasar ta ba tare da wata tsangwama ba

JEDDAH – Jiragen da ke fitowa daga Isra’ila yanzu za su iya shiga kasar Saudiyya yayin da Masarautar ta dage dokar hana jiragen Isra’la jigila a kasar.
A baya -bayan nan Saudiyya ta hana jiragen da suka fito daga kasar Isra’ila jigila a kasar ta.
Jiragen da ke jigila a yanzu za su iya shawagin shige da fice a kasar Saudiyya, a wani mataki na maraba da shugaban Amurka Joe Biden ya yi wanda a yanzu haka ya keshirin kai ziyara a kasar ta Saudiyya a ranar Juma’a.

Bayan yarjejeniya Kasar Saudiyya ta bude tashan jirgin saman ta ga Isra’ila

Dangane da yarjejeniyoyin kasa da kasa, Saudiyya a yanzu ta bude kafofin jigilar jiragen sama ga dukkan farar hula sakamakon cika sharuddan kasar dangane da abinda ya shafi harkar jirage.
A cewar GACA, shawarar za ta kara haɓaka haɗin harkar jirage na ƙasa da ƙasa tare da ƙarfafa matsayin Masarautar a matsayin cibiyar duniya mai haɗa nahiyoyi uku.

Jiragen isra’ila suna kewaye saudiyya

Yawancin jiragen da ke shige da fice daga Isra’ila,sai dai su kewaye Saudi Arabiya wanda hakan ya kara tsayin lokacin tashin jirage da kuma karuwar man fetur.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba da wannan matsaya a matsayin muhimmin mataki na gina ingantaccen haɗin kai da kwanciyar hankali a bangaren Gabas ta Tsakiya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe