37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda wani mutum ya baiwa wata mabaraciya katin bankin sa na ATM ta ciri iya kudin da take so 

LabaraiYadda wani mutum ya baiwa wata mabaraciya katin bankin sa na ATM ta ciri iya kudin da take so 

Mutane da dama sun yabawa wani mutum, bayan wani bidiyo da yake yawo a yanar gizo, ya nuna haska  mutumin ya nuna soyayyar sa ga wata mabaraciya. 

Yadda mutumin ya ga mabaraciyar

Mutumin wanda aka bayyana sunan sa da Ryan Tama, ya je wurin cirar kudi na ATM ne, sai ya ga wata matashiya a loko, tana barar neman taimakon sadaka. 

A cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na TikTok, anga marubucin ya tunkari wannan matashiya, inda ya mika mata katinsa na cirar kudi, kuma ya bata wuka da nama, cewa ta ciri ko nawa take so. 

A fadar mutumin, shi bashi da canjin kananan kudi wadanda zai iya bata, a sakamakon haka sai ya yanke shawarar ya bata katin baki daya. 

Matashiyar mabaraciyar ta yi mamaki

Matashiyar ta kalleshi cikin mamaki, amma kawai sai ta aiwatar da abin da ya bata umarni, inda ta sanya katin a cikin injin cire kudin, kuma ta ciri abin da take so. 

Bayan ta cire kudaden, sai mutumin ya karbi katin sa, kuma ya jadda wa matashiyar nan cewa, kudin da ta cire, nata ne. 

Cikin yanayi na rudewa, da rashin sanin me zatayi, matashiyar mabaraciyar ta godewa mutumin, saboda halin kirkin da ya nuna mata. 

Martanin mutane ga wannan mutum

King Omar, yace :

“Da kyau dan uwa, ina sonka, ” Saboda ka taimaki yar uwar mu wadda take bukatar taimako, Allah ya baka linkin ba linkin. “

Wasimbrown yace,

” Allah ya kare ka, ya baka karko irin wanda yake baiwa wadanda suka yi kyakkyawan aiki”

Yo, ya ce :

” Kai mutumin kirki ne, ina fata ka sami sama da abin da ka bayar, Saboda taimakon mabukata.” 

H, yace,

” Ni kuma a gani  na, an ci zarafin ta, saboda yana dauka a bidiyo ne, idan za’a yi abu mai kyau ba sai an yada ba. “

Hukumomi sun saki mabaraciya Hadiza Salisu da aka kama da kudi sama da N500k a Abuja

Hukumar dake kula da babban birnin tarayya Abuja ta wanke Hadiza Ibrahim mai shekaru 48, wacce ta shahara wajen bara akan tituna, wacce aka damke ta da kudi Naira N500, 000 da dala 100.

Sun bayyana cewa bata daga cikin duk wata alaka da ta danganci safarar miyagun kwayoyi, siyar da makamai, garkuwa da mutane da dai sauran munanan laifuka. Hukumar ta ce kudaden da aka samu Hadiza da su ta dade tana tara su

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe