28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Tsananin kishi yasa matar aure babbake mijinta, ƴan sanda sun bazama neman ta

LabaraiTsananin kishi yasa matar aure babbake mijinta, ƴan sanda sun bazama neman ta

Ƴan sanda a jihar sun bazama neman wata matar aure mai suna Ifeoluwa Bamidele, ruwa a jallo, wacce ake zargin ta cinnawa mijinta mai suna Bolu, wuta a Osogbo babban birnin jihar ranar Lahadi.

Kakakin hukumar ƴan sandan ta jihar, SP Yemisi Opalola, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Osogbo. Jaridar Daily Trust ta rahoto

Ƴan sanda sun ce an kawo batun yunƙurin kisan kai da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare a ranar Lahadi.

Da misalin ƙarfe 11:30 na dare, ana zargin matar wani mai suna Bolu, da cinna masa wuta.

An tafi da mijin zuwa asibiti

An garzaya da wanda abin ya ritsa dashi zuwa babban asibirin Osogbo, inda daga nan aka tura shi zuwa asibitin University College Hospital, Ibadan (UCH) domin samun kulawa mai kyau

Kakakin ƴan sandan tace hukumar su za ta tabbatar cewa an cafko matar auren.

Ana zargin cewa Bamidele ta aikata wannan ɗanyen aikin ne bayan ta gano cewa mijinta yaci amanar ta inda har ya haifi da wata mata a waje bada aure ba.

Sai da ta shirya tsaf kafin aikata wannan ɗanyen aikin

Matar auren ta kuma bar wani saƙo a manjahar Whatsapp, wanda yake nuni da cewa sai da ta shirya tsaf kafin aiwatar da wannan mummunan aikin.

Saƙon na cewa:

Ni na kasance a koda yaushe natsatstsiyar yarinya, sannan ban taɓa aikata hakan ba a rayuwata amma Teebam (mijinta) ya kai ni maƙura.

A wannan datsin, duk sai kun yi mana kuka dani da shi kafin wayewar gari. Nayi muku alƙawarin hakan.

Bidiyo: Yadda tsananin kishi ya sanya mijina ya cire min ido da ‘yan yatsu -Wata matar aure

A wani labari na daban kuma wata matar aure ta bayyana yadda mijinta ya cire mata idon da ƴan yatsu.

Wata mata mai suna Maureen Atieno Omolo, ta bayyana yadda mijinta ya cire mata ido, ya datse mata ‘yan yatsu sannan yaji mata raunika da adda da dama a jikinta.

Da take tuno mummunan lamarin a wata hira da Afrimax TV, matar tace niyyar mijinta a lokacin shine ya halaka ta a maimakon ya rasa ta ga wani namijin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe