
Ya tara kudi na tsawon shekaru 43
Zuwa Makkah domin yin aikin Hajji, shi ne burin kowane musulmi. Ga labarin wani mutum da ya dinga tara kudi kusan shekaru 43 domin cikar burinsa na ziyartar dakin Allah.
Ya tara kudinsa tsawon shekaru 43 don yin aikin Hajji. Bai yi kasa a gwiwa ba ya cigaba da tara kudi na tsawon wannan lokaci saboda kwadayin yin aikin Hajji.
Ya sayar da filinsa don yin aikin Hajji
Harkazalika bai tsaya nan ba , wannan mutumi ganin bai bai da isassun kudi da za su kaishi Makka don aikin Hajji. Kasancewar yana da wani fili sai kawai ya sayar wa abokinsa, wanda daga baya ya yi aiki a wannan filin domin ya karasasa tanadan kudin aikin Hajjinsa.
Lokaci ya shude,bayan gwagwarmayar shekaru 43, wannan dattijo ya yi nasarar hada isasshen kuɗi don yin aikin Hajji. Lallai wannan lamarine mai matukar ban tausayi.
Ya amsa kiran mahalicci inda aka same shi kwance a kan hannunsa na dama rai yayi halinsa . Yadda ya dade yana burin zuwa dakin Allah sai gashi rai ya yi halinsa.
Wata Mahajjaciya ta rasa ranta sa’o’i kadan bayan dawowarta daga Arfah
A wani rahoton kuma Hukumar Alhazai ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar Hasiya Aminu, wata ‘yar jihar Kaduna.
Ta rasu ne tana tsaka da barci jim kadan bayan ta dawo daga dutsen Arafat, kamar yadda makwaftan da ke cikin tanti suka bayyana.
Shugaban aiyuka wanda ya kasance shugaban ma’aikatan lafiya na Najeriya, Dr Usman Galadima, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa ba a san musababin abinda ya yi sanadin mutuwar ta ba.
Ya ce tuni aka sanar da iyalan Hasiya Aminu rasuwarta kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hasiya Aminu ita ce mahajjaciya ta uku da ta rasu a aikin Hajjin 2022.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com