31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

‘Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan 

Ilimi'Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami'ar Portsmouth dake birnin Landan 

Mai martaba tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido, tare da mai martaba sarkin Zazzau ambasada Nuhu Bamalli, sun halarci bikin kammala karatun dan tsohon sarki Sunusin, mai suna Mustapha Lamido Sanusi.

Sakamakon da dan sarki Sunusi Lamidon ya samu

sunusi lamido
‘Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan 

An tattara rahoton cewa, Mustapha din ya fita da sakamako ajin farko, wato (first class ) a fannin ilimin tattalin arziki, a wata jami’a Portsmouth dake birnin Landan. 

A lokacin bikin, sarkin yayi kira ga yaron da ya kammala digirin, da yayi amfani da ilimin nasa wajen samar da  cigaba da  tallafawa marasa karfi. 

Dalilin neman ilimi , inji sarki Sunusi

sunusi lamido
‘Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan 

A fadar sa, yace babban dalilin da yasa ake yin ilimi shine domin  a kyautata gobe, da kuma yin hidima ga al’umma. 

Da take nagana a yau, sarkin ya ce, Mustapha din  ya yi nuna hazaka da ta daga darajar Najeriya, inda ya kara da cewa, dukkanin dalibai da suke karatu a kasashen waje, suyi Koyi da shi domin su fita da kyakkyawan sakamako. 

sunusi lamido
‘Dan tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido ya fita da ajin farko (First Class ) a jami’ar Portsmouth dake birnin Landan 

Da yake nuna farin cikin sa, Malam Mustapha din, ya gode musu tare da yin murna, saboda karamcin da suka nuna masa.

A karon farko Sanusi Lamido zai kai ziyara jihar Kano tun bayan tsige shi daga sarauta

Masu ruwa da tsaki akan harkokokin siyasa da tsaro sun nuna damuwar su akan ziyarar da tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya ke shirin kaiwa jihar. Kano.

Waɗansu daga cikin masu ruwa da tsakin da su kayi magana da jaridar LEADERSHIP sun roƙi tsohon sarkin da ya haƙura da ziyarar da ya ke son kawowa saboda gudun samun rikici tsakanin magoya bayan sa da kuma masu adawa da shi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe