34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Dole na kalubalanci alamomi uku na musulunci a kotu ; cire rubutun Arabi a jikin Naira, rubutun Kurani a jikin kayan sojoji da kuma saka Hijabi ga mata ‘yansanda – Lauya Malcolm

LabaraiDole na kalubalanci alamomi uku na musulunci a kotu ; cire rubutun Arabi a jikin Naira, rubutun Kurani a jikin kayan sojoji da kuma saka Hijabi ga mata 'yansanda...

Lauya dan rajin kare yancin dan Adam , Malcolm Omirhobo, ya kara jadda matsayar sa ta tsaiwar gwamen Jaki akan sai ya ga bayan wadansu alamomi uku na musulunci a alamuran al’umma a Najeriya a gaban kotu. 

Kungiyar musulunci ta nemi da ya janye tuhumomin

Wata kungiya da take rajin goyon baya ga addinin musulunci da bin harkokin sa, da aka fi sani da MURIC, ita ce ta bukaci lauya Omirhobo din da ya janye aniyar sa ta kalubalantar rubutun Arabi a jikin Naira, sanya hijabi ga mata ‘yansanda da kuma rubutun Kurani a jikin kayan sojoji, idan dai har shi ba kiyayya yake nunawa ga musulunci da musulmai ba. 

Malcom Omirhobo 531x299 1 1
Dole na kalubalanci alamomi uku na musulunci a kotu ; cire rubutun Arabi a jikin Naira, rubutun Kurani a jikin kayan sojoji

Da yake mayar da martani, lauyan wanda aka fi gane shi da shigar sa ta addinin sa na gargajiya, zuwa kotu; ya ce, shi ba zai saurari kiraye-kirayen MURIC din ba, “saboda kyasa-kyasan da yake korafi akan su, na al’umma ne gaba daya, domin a samu dorewar kasar da ba’a fifita wani addini ba domin tabbatuwar Najeriya daya”. 

Jawabin lauyan akan tuhumar alamomi ukun na musulunci

” Na gani, kuma na karanta rubutun da MURIC suka yi, ta karkashin shugaban ta kuma shugaban kwamatin amintattun ta mai suna  Farfesa Ishaq Akintola, inda suke neman na janye tuhumomi uku da nakeyi, wanda nayi roko da sashe na 10 na kundin tsarin mulkin Nageriya, wanda yake magana akan cire addini a tsarin mulki, wanda kuma ya zama hujja a gareni cewa ba kiyayya nake nunawa ga musulunci da musulmai ba, kuma Ni bama ni da ra’ayin nuna kiyayyar addini. 

Alamomi ukun sune kamar haka

Tuhumomi ukun da farfesan yake nufi, sune ;

Rubutun Arabi a jikin Naira, sanya hijabi ga mata ‘yansanda musulmai da kuma rubutun Kurani a jikin kayan sojoji. 

” Bazan janye wadannan tuhumomi ba, saboda basa nuna wata kiyayya ga musulmai da musulunci, kamar yadda MURIC suke so su nuna wa musulmai domin su yarda da hakan, tuhumomin suna kare muradun yan kasa ne gaba daya, saboda a sami dorewar kasa daya wadda ba’a fifita wani addini ba, domin cigaban Najeriya “. Omirhobo din ya fada a wani jawabi.

” A kan shiga ta da naje babbar kotu da ita, da kuma kotun koli, banga abin da ya shafi MURIC ba, shiga ta yanci na ne, na tunani, walwala da kuma addini, babu inda aka hana ni, matukar ban shiga hakkin wani ba. In dai kuwa ban shiga hakkin kowa ba, kuma ban taka dokar kasar Najeriya ba, babu wanda ya isa ya hana ni yanci na, koda kotu ce, kai ko da shugaban kasar Nageriya ne”. 

“Ina shawartar MURIC da tayi wa’azi akan Soyayya ba kiyayya ba. Ku dena dora musulmai akan sauran addinai da kabilu a Najeriya. Ku dena nuna kin wasu bangare, ku zama masu yakana da bin doka.

Kamar yadda ya fada

Da ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta amince ɗalibai musulmai sanya hijabi a makarantun jihar Legas

Kotun ƙoli ta tabbatar da ‘yancin da ɗalibai mata su ke da shi a jihar Legas na sanya hijabi ba tare da nuna mu su wariya da tsangwama. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An tabbatar da hukuncin damar sanya hijabi a makarantun jihar Legas

Kotun ƙolin ta tabbatar da wannan hukuncin ne yau Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Alƙalan da su ka saurari ƙarar dai sun haɗa da, mai shari’a Olukayode Ariwoola, Justice Kudirat Kekere-Ekun, mai shari’a John Inyang Okoro, mai shari’a Uwani Aji, mai shari’a Mohammed Garba, mai shari’a Tijjani Abubakar, da mai shari’a Emmanuel Agim

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe