34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Hukumar lafiya ta Kasar Ghana ta kebe mutane 98 da suka kamu da cutar Marburg

LabaraiHukumar lafiya ta Kasar Ghana ta kebe mutane 98 da suka kamu da cutar Marburg
Bats structures organs sound frequencies signals contexts 750x375 1

Hukumar lafiya ta Ghana (GHS) ta tabbatar da bullar cutar Marburg inda aka samu mutane 2 dauke da wannan cutar, cuta Marburg cuta ce mai saurin yaduwa a cikin iyalai kamar cutar Ebola.
Wannan na zuwa ne bayan samun bullar cutar na farko a yankin Ashanti a ranar 7 ga Yuli, 2022, wanda Cibiyar lafiya ta Tunawa da Noguchi ta kasar ta yi bincike akai.
An aika da sakamakon zuwa cibiyar Pasteur da ke Dakar (IPD) na kasar Senegal, tare da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) inda aka tabbatar da cutar Marburg ce.
Majinyata biyun wanda sun fito ne daga yankin kudancin Ashanti – wanda cutar ta yi sanadiyar rayuwar su k da dai ba ‘yan uwa ba ne– alamomin cutar sun hada da gudawa, zazzabi, tashin zuciya da amai. An kai su wani asibitin gunduma a yankin Ashanti,” in ji hukumar ta WHO a cikin rahoton da suka bayar.
Shugaban GHS, Patrick Kuma-Aboagye, ya bayyana cewa mutane 98 da aka gano a matsayin wadanda suka kamu da cutar a yanzu haka an keɓe su, ya kara da cewa “wannan shine karo na farko da Ghana ta tabbatar da cutar Marburg.”
Da yake tabbatar da ci gaban, darektan hukumar ta WHO a Afirka, Matshidiso Moeti, ya ce “Hukumomin kiwon lafiya sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fara shirye-shiryen yiwuwar barkewar cutar.”

Mawaki Idris Abdulkareem ya bayyana matsanancin halin da yake ciki daga kan gadon jinyar sa na asibiti
A wani rahoton kuma Shahararren mawakin nan na Najeriya Idris Abdulkareem, ya yada sabon bidiyo daga gadon sa na asibiti, inda ya bayyana matsanancin ciwon da ya addabeshi, a ranar Laraba, shida 6 ga watan Yuli.
Matsanancin ciwon koda ne yake damun sa
Ya bayyana cewa, yana fama da matsanancin ciwon koda, wanda a halin yanzu yake karkashin kulawar likitoci, a wani asibiti dake jihar Legas.

A cikin bidiyon da ya saki, Idris din ya godewa daukacin jama’a, saboda nuna damuwar su da abin da ya same shi, tare da nuna kwarin gwiwa gareshi, inda yace yana kara samun sauki daga matsanancin ciwon da ya same shi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe