
Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano a ranar Talata, ta yi watsi da umarnin wucin gadi da tun farko ta bayar na hana gwamnatin jihar Kano karbo aron kudi kimanin Naira biliyan 10.
Dokta Yusuf Isyaka-Rabiu, Darakta-Janar na gamayyar kungiyoyin sa-kai na Kano First Forum, KFF ne ya shigar da karar yana neman don a dakatar da gwamnatin jihar Kano karbo rancen naira biliyan 10.
Wadanda ake kara sun hada da Gwamna, Babban Lauyan Jihar Kano, Kwamishinan Kudi na Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Sauran sun hada da Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar Kula da Kudi.
Da farko dai kotun ta hana gwamnati Kano ciyo bashin kudin don siyo na’urar CCTV, na’urorin ana amfani da su ne wurin daukar hoto don sanin halin da halin da gari yake ciki.
Ganduje ya bayyana muhimmin dalilin da yasa Tinubu ya ɗauki musulmi a matsayin mataimaki
A wani rahoton Kuma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi musulmi ne a matsayin abokin takarar sa domin kawar da muhimmanci na musamman da ake ba addini a siyasar Najeriya
Ganduje wanda yana a gaba-gaba cikin masu yaƙin neman zaɓen Tinubu, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana da ƴan jarida a masallacin Juma’a na Unguwar Sabo, a Osogbo, babban birnin jihar Osun. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ganduje ya lissafo matsalolin da Najeriya ke fama da su
Yace manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta sune tattalin arziƙi, rashin aikin yi da sauran wasu abubuwan cigaba ba addini ba.
Ganduje ya bayyana cewa:
Mun bashi shawara (Tinubu) ya zaɓi musulmi domin kawo ƙarshen batun addini da ake nuna wa a siyasar Najeriya
Mu gwamnonin arewa mun tsaya tsayin daka cewa dole ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga kudu domin kawar da waɗannan bambance-bambancen.
Ganduje yana a jihar Osun ne a matsayin mataimakin shugaban kwamitin zaɓen jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar na ranar Asabar.
Ɗaukar musulmi da Tinubu yayi a matsayin mataimakin sa ya jawo cece-kuce sosai a sassa da dama na ƙasar nan, inda wasu suke ganin hakan da ɗan takarar yayi sam bai dace ba.
Mutane da dama sun yi tofin Allah tsine akan wannan matakin da ɗan takarar ya ɗauka, yayin da wasu da dama suka nuna goyin bayan su inda suke cewa cancanta da nagarta sune abinda ake buƙata a wurin ɗan takara ba wai addinin sa ba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com