Wata dirarriyar budurwa wacce ke sana’arta ce siyar da ruwan leda da na gora tare da lemuka ta koka akan yadda hankalin samari ya fi karkata akanta maimakon kayan sana’arta, Amihad.com ta ruwaito.
Tana sana’ar ne birnin Accra da ke kasar Ghana don ta rufawa kanta asiri, amma abinda ya fi ci mata tuwo a kwarya shi ne yadda aka fi neman lambar wayarta.
Mai sayar da ruwan ba wata bace face Nina Ricchie, wata fitacciyar mawakiyar a Ghana wacce tayi bad da kama don gano masu munanan dabi’u a cikin mutane da ke lalata yara mata musamman masu tallace-tallace a titina.
Kamar yadda ta bayyana a shafinta na Instagram, ta fuskanci kalubale musamman daga wurin samari bayan fitarta tallar na sa’o’i kadan.
A wannan dalilin ne yasa ta bayyanawa iyaye irin matsalolin da ke tattare da daurawa yaransu tallace-tallace musamman yara mata.
‘Yan mata da dama su kan buge da tallata kansu maimakon kayan sana’ar da aka daura musu.
Kano: Daga zuwa siyo mata Shawarma, budurwa ta tsere da motar saurayinta
Jami’an ‘yan sanda sun yi ram da wata budurwa bayan ta tsere da motar saurayinta wanda ya fito siyo mata Shawarma a Unguwar Kofar Famfo da ke Birnin Kano, Aminiya ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai yadda komai ya wakana.
Kamar yadda Kiyawa ya shaida, saurayin da aka sacewa motar ya ce a ranar 12 ga watan Yulin 2022 budurwar ta tsere masa da motar.
‘Yan sanda sun samu nasarar kama budurwar mai suna Ilham kuma ta shaida musu cewa tana bin saurayin nata bashin N150,000 ne wanda take kyautata zaton ba zai biya ta ga.
Ta ce hakan ne yasa ta yanke shawarar sace masa mota. Sai dai saurayin ya musanta wannan batu nata inda yace ta waya su ka hadu.
Ya ce bayan nan ne su ka hadu a Hauren Wanki wanda daga nan ta ce tana son cin Shawarwa don yunwa take ji.
Ya ce dawowarsa ke da wuya ya nemi motarsa ya rasa.
A bangaren Ilham kuwa ta ce wani saurayinta ta kira don ya tuka mata motar gida don ya ajiye mata motar a gidansu har sai ta amshi kudinta a hannun saurayin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com