24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Gwamnatin Malaysia ta haramta auren macen da bata kai shekaru 18 ba

LabaraiGwamnatin Malaysia ta haramta auren macen da bata kai shekaru 18 ba

Majalisar dokokin Kedah da ke Malaysia ta gyara tsofaffin dokokin kasar dangane da auren musulmar da bata kai shekaru 18 ba, LIB ta ruwaito.

Yayin bayani a zaman majalisar na wannan makon, kakakin majalisar, Datul Juhari Bulat ya ce za ayi gyara dangane da dokar kara yawan shekarun auren yara mata musulmai, daga 16 zuwa 18 tare da bayar da horaswa ga duk namijin da ya kara aure ba tare da ya nemi izinin kotu ba.

Horaswar za ta kasance daurin shekara daya ko kuma biyan tarar RM3,000 a maimakon daurin gidan yari na watanni 6 ko kuma biyan tara ta RM1,000..

A cewarsa:

“Idan mutum yana son yin aure amma akwai wata matsala, zai iya neman yardar kotu, idan kotun ta gano cewa ka cancanci yayi auren ko da kuwa macen da zai aura shekarunta 16, za ta iya aure bisa amincewar kotun.”

Datuk ya ci gaba da bayyana cewa duk mace musulmar da bata kai shekaru 18 da haihuwa ba kuma tana son yin aure za ta iya neman amincewar kotu.

Ya ci gaba da bayyanawa manema labarai cewa:

“Idan kotun ta yarda da cancantar wacce ta nemi izinin ta yi aure, ko da kuwa shekarunta 16, za ta iya yin aurenta bisa izinin kotun.

“Za a ci tarar wadanda su ka kara aure ba tare da neman izinin kotu ba.”

Juhari ya kara da cewa majalisar ta amince da batun kara yawan kudin tarar daga RM1,000 da daurin watanni shida ga wadanda su ka kara aure ba tare da amincewar kotu ba zuwa RM3,000 da daurin shekara daya a gidan gyaran hali.

An haramtawa mazan Saudiyya auren mata ‘yan ƙasashen waje

An dakatar da mazan Saudiyya auren mata daga ƙasashen Pakistan, Bangladesh, Chad, da Burma. An dai sanar da wannan sabon matakin ne domin a hana mazan na ƙasar ta Saudiyya auren mata ‘yan ƙasashen waje.

Ana buƙatar mazan Saudiyya masu son auren mata ‘yan ƙasashen waje da su nemi iznin hukumomi

Jaridar Lifeinsaudiarabia.net ta rahoto cewa duk wani ɗan Saudiyya da ya ke son auren ‘yar ƙasar waje, dole sai ya nemo izni daga hukumomin gwamnati sannan ya miƙa takardar neman aure a wurin hukumomin da su ka dace.

Darektan ‘yan sandan birnin Makkah, Major General Assaf Qureshi, ya bayyana cewa duk iznin neman aure wanda baa cikin Saudiyya zaa yi shi ba, yana bin tsare-tsare da hanyoyi masu tsauri kafin a amince ko kuma ayi watsi da shi.

Ana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a bayar da sakamakon iznin neman auren mata ‘yan ƙasasjen waje

Kwamitin ne yake da alhakin amincewa ko watsi da iznin neman auren. Haka kuma, domin a yanke hukunci mai kyau, kwamitin yana buƙatar lokaci mai tsawo wajen yin aiki akan iznin neman auren.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe