Jami’an ‘yan sanda sun yi ram da wata budurwa bayan ta tsere da motar saurayinta wanda ya fito siyo mata Shawarma a Unguwar Kofar Famfo da ke Birnin Kano, Aminiya ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai yadda komai ya wakana.
Kamar yadda Kiyawa ya shaida, saurayin da aka sacewa motar ya ce a ranar 12 ga watan Yulin 2022 budurwar ta tsere masa da motar.
‘Yan sanda sun samu nasarar kama budurwar mai suna Ilham kuma ta shaida musu cewa tana bin saurayin nata bashin N150,000 ne wanda take kyautata zaton ba zai biya ta ga.
Ta ce hakan ne yasa ta yanke shawarar sace masa mota. Sai dai saurayin ya musanta wannan batu nata inda yace ta waya su ka hadu.
Ya ce bayan nan ne su ka hadu a Hauren Wanki wanda daga nan ta ce tana son cin Shawarwa don yunwa take ji.
Ya ce dawowarsa ke da wuya ya nemi motarsa ya rasa.
A bangaren Ilham kuwa ta ce wani saurayinta ta kira don ya tuka mata motar gida don ya ajiye mata motar a gidansu har sai ta amshi kudinta a hannun saurayin.
An kama saurayin nata wanda ya taya ta satar motar don ci gaba da bincike.
Saurayi ya halaka budurwar sa bisa ragargaza masa wayar iPhone
Ƴan sanda a jihar Delta sun cafke wani saurayi, Godspower Adigheti, mai shekaru 23, bisa halaka budurwar sa, Gift Ojoku.
Jaridar The Punch ta tattaro cewa Adigheti ya halaka Oloku, wacce ɗaliba ce a makarantar koyon fasaha ta jihar Delta, bisa lalata masa wayar iPhone 11 Pro Max.
Yadda saurayin ya halaka budurwar ta sa
Lamarin ya auke ne a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli 2022, a Ozoro, cikin ƙaramar hukumar Isoko ta Arewa a jihar.
An samo cewa Adigheti da budurwar ta sa sun samu kace-nace ne wanda ya rikiɗe zuwa faɗa a tsakanin su.
Wata majiya ta bayyana cewa budurwar tana rayuwa ne tare da wanda ake zargin kuma akwai yarinya a tsakanin su.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com