34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Saurayi ya halaka budurwar sa bisa ragargaza masa wayar iPhone

LabaraiSaurayi ya halaka budurwar sa bisa ragargaza masa wayar iPhone

Ƴan sanda a jihar Delta sun cafke wani saurayi, Godspower Adigheti, mai shekaru 23, bisa halaka budurwar sa, Gift Ojoku.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa Adigheti ya halaka Oloku, wacce ɗaliba ce a makarantar koyon fasaha ta jihar Delta, bisa lalata masa wayar iPhone 11 Pro Max.

Yadda saurayin ya halaka budurwar ta sa

Lamarin ya auke ne a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli 2022, a Ozoro, cikin ƙaramar hukumar Isoko ta Arewa a jihar.

An samo cewa Adigheti da budurwar ta sa sun samu kace-nace ne wanda ya rikiɗe zuwa faɗa a tsakanin su.

Wata majiya ta bayyana cewa budurwar tana rayuwa ne tare da wanda ake zargin kuma akwai yarinya a tsakanin su.

Majiyar ta bayyana cewa:

Ta fita ne bayan ta dawo gida, saurayin ya nemi sanin daga ina take.

A cikin hakan ne, faɗa ya barke a tsakanin su sannan budurwar ta lalata masa allon wayar sa ƙirar iPhone 11 Pro Max. Hakan ya sanya ya sassareta da adda.

Hukumomi sun tabbatar da aujuwar lamarin

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Ya bayyana cewa:

A ranar 16 ga watan Yuli, 2022, DPO mai riƙe da Ozoro ya samu kiran gaggawa cewa wani saurayi Godspower Adigheti, mai shekaru 23, mai zama a Oramudu kwatas, ya jiwa budurwar sa Gift Oloku, mai shekaru 22, raunika da adda. An garzaya da budurwar zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwar ta. A halin da ake ciki, wanda ake zargin yana a tsare yayin da ake cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Saurayi ya halaka budurwarsa, ya kira ‘yan uwanta ya sanar musu sannan ya cika wandonsa da isa

A wani labarin kuma, saurayi ya halaka budurwar sa sannan ya sanar da ƴan’uwanta kafin ya cika wandon sa da iska.

Ana zargin wani saurayi da kashe budurwarsa a Abuja, ya kuma sanar da ‘yan uwanta cewa “su zo su dauki gawar ta”.

A watan Mayun 2021, kuma ya shiga cikin watan Agusta na wannan shekarar, an bayyana cewa wanda ake zargin ya koma gidan marigayiyar ne saboda ba shi da aikin yi kuma ba shi da wurin kwana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe