Wadannan jerin sunaye da hotunan jarumai sun musulunta ne wasu don ra’ayin kansu .Wasu kuma saboda sun auri mazaje musulmai .
Ga jerin sunayen mata jaruman da suka musulunta
1) Akindele Funke.

Funke Akindele, ta musulunta ne bayan ta auri Alhaji Kehinde Almaroof Oloyede, wanda aka daura auren a ranar 24 ga watan Mayu 2012, sabida Oloyede musulmi ne, ita ma Funke sai ta musulunta, ta canja sunan ta zuwa Khadijat.
2. Liz Da Silva

Sananniyar jaruma da aka fi sani da Liz Da Silva, ta taso a matsayin cikakkiyar kirista, har sai da ta haifi danta na fari da wani musulmi da ba’a tantance waye ba, amma dai ana kiransa da suna Olaoye. Bayan ta haifi dan nasu ne, sai Lizzie din da danta suka canja addini suka koma musulunci, inda ta canja sunan ta zuwa Ai’shat.
3. Lizzy Anjolin

Jarumar fim Elizabeth Anjorin, wadda kuma ake kira Lizzy Anjolin, ta kasance a da kamar yadda sunanta ya nuna, ta taso, a cikin al’ummar kirista, amma daga baya sai ta koma musulunci domin radin kanta, saboda tace addinin yana burgeta. Ta canja sunan ta izuwa Sakinat da Aishat, inda ta canja sunan yar ta, kuma ya koma Rufaida.
4. Fathia Balogun

Ita jaruma Fathia Balogun, ta tashi ne a gidan da suke bin, darikar cocin Roman Katolika. Bayan ta yi imani da wadansu mala’iku na kusa da Allah, kamar yadda suke da imanin hakan, daga karshe kawai sai ta karbi addinin musulunci. Ta canja sunan ta zuwa Fatiha, kafin daga bisani ta auri wani darakta mai suna Said Balogun.
5. Mercy Aigbe

Kazim Adeoti da Mercy Aigbe, sunyi auren su ne a kebance, ance Mercy din itace ta nuna sha’awar ta ga auren mijin nata, wanda aka ce ya taba auren wata matar. Kamar mijin nata Mercy din ta musulunta, inda sunan ta ya koma Minna.
6. Bimpe Mo

Mata ga jarumin fim din kudu mai suna Latif Dimeji, ta musulunta ne a karshen shekarar da ta wuce, bayan auren su da jarumin. Kafin ta auri jarumin ita cikakkiyar kirista ce wadda bayan ta aure shi ta canja addinin ta ya koma musulunci.
Mo Bimpe ta Musulunta bayan ta auri Musulmi ta canja sunanta zuwa Rahmatullah
Wani rubutu da jarumi Adedimeji Lateef ya wallafa a shafin shi na kyakkyawar amaryar shi Mo Bimpe ya nuna cewa tuni jarumar ta canja sunanta zuwa na Musulmai.
A baya dai jarumar tana bin addinin Kiristanci sau da kafa, amma sakamakon auren jarumin da tayi wanda yake shi Musulmi ne ya sanya ta canja addini zuwa addinin Musulunci.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com