31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Hausawa mazauna kasar Sudan sun gudanar da zanga-zanga bisa kisan ‘yan uwansu da aka yi

LabaraiHausawa mazauna kasar Sudan sun gudanar da zanga-zanga bisa kisan 'yan uwansu da aka yi
7188dd8d 4d35 488d b697 4bab7ae67e0b

Hausawa mazauna Kasar Sudan sun gudanar da zanga-zanga a biranen kasar, don nuna bacin ransu, game da kisan da aka yi wa ‘yan uwansu a rikicin kabilancin da ya barke ‘kwanakin baya a kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin mutane 79 ne aka kashe sakamakon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berti a jihar Blue Nile.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa daruruwan Hausawa ne suka fito zanga-zangar a Khartum babban birnin kasar rike da takardu da ke dauke da rubutun suna neman a yi adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe.

Yajin aiki: Kungiyar NUPENG ta yi alkawarin ba da goyon baya ga zanga-zangar da kungiyar kwadigo ta shirya game da rufe jami’o’in Najeriya

A wani rahoto kuma Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, NUPENG, ta goyi bayan zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya yi kan yajin aikin da malaman jami’o’in (ASUU) ke ci gaba da yi.
Shugaban NLC, Ayuba Wabba, a ranar 1 ga watan Yuli, ya ce NLC za ta fara zanga-zanga a fadin kasar idan har yajin aikin ya ci gaba.
Yajin aikin ASUU dai ya shafe kusan watanni biyar kenan tun bayan fara yajin aikin a ranar 14 ga watan Fabrairu.
Sauran kungiyoyin ma’aikata a fadin jami’o’in kasar su ma sun bi sahun yajin aiki inda komai na harkar ilimi ya tsaya chak.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta NUPENG ta fitar, ta yi Allah-wadai da halin da gwamnati ke ciki na rashin neman mafita mai dorewa kan yajin aikin da ake yi.
Don haka, ta yi nuni da cewa, “manyan mambobin kungiyar NUPENG sun goyi bayan matsayar da NLC ta dauka na nuna rashin amincewa da halin da ake ciki a bangaren ilimi, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen shiga yajin aikin da ake shirin yi a fadin kasar kan lamarin.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe