27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Wata mata ta sayawa mijin ta ‘yar bebin roba domin ta dinga maye gubinta idan bata nan

LabaraiWata mata ta sayawa mijin ta 'yar bebin roba domin ta dinga maye gubinta idan bata nan

Wata mata da take matukar son mijin ta ,mai suna Char Gray ‘yar kasar Burtaniya ta sayawa mijin ta wata ‘yar bebin roba, wacce aka sa mata suna Dee, domin ta gamsar da mijin ta mai yawan sha’awa idan bata nan.

Dalilin sayen ‘yar bebin robar

A fadar Coventry Telegraph, Grey din , ta yanke shawarar sayan ‘yar bebin ne bayan mijin nata mai matukar sha’awa , wanda akabayyana sunan sa da Callum, ya shawararceta akan zai karo wadansu mata guda uku, waɗanda ita kuma sam ba ta gamsu da su shigo rsyuwsr su ba.

yar bebin roba

A maimakon ta aminta da a kawo su, sai ta sanya makudan kudi har , Naira 747,112.50 ta sayi wannan ‘yar tsana mai kama da ita ,domin mijin nata ya dinga saduwa da ita a madadin ta idan bata nan, a madadin ya kawo wasu mata uku masu halittar mutum na gaske .

Abin da mijin nata ya fada akan ‘yar tsanar

Da yake nuna jin dadin sa , a wata kafar yada labarai ta Southwest, Callum Gray, ya ce wannan ‘yar tsana bawai kadai gamsuwa take bashi ba, har ma da shakuwa.

“Dee ba kawai ‘yartsana ba ce, ta kasance abar shakuwa sosai a garemu. Ta taimaki ƙarfafawar dangantakarmu kuma tana gamsar da rayuwar mu ta mu’amalar huldatayyar aure. ”

Wata mata ta maka mijin ta a kotu saboda ya auro aminiyar ta a matsayin kishiya a gareta 

Wata mata matashiya ‘yar shekara 25 mai suna Firdausi Musa, ta maka tsohon mijin ta mai suna Saidu Abubakar a kotu, a garin Kaduna, saboda ya auro mata aminiyar kawar ta a matsayin kishiya. 

Da take bayani, lauyar mai karar, mai suna Zainab Murtala, ta ce, mijin matar ya kwashe kayan ta dake cikin akwati da sauran kyaututtukan da ya bata, duk ya mallakawa sabuwar amaryar ta sa. 

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe