27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutar lantarki

LabaraiDa duminsa: Gwamnatin tarayya ta sake kara farashin wutar lantarki
  • Bisa umarnin NERC, ‘yan Najeriya za su fara biyan sabon farashin wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Janairu
  • Farashin ya tashi kwarai sakamakon yadda tsadar rayuwa da kuma karayar darajar kudi ya auku a Najeriya
  • NERC ta ce za ta kara duba akan sabon farashin ne idan har hukumar ta kara bayar da wani umarnin

A bisa umarnin da aka bayar a ranar 31 ga watan Disamban 2020, wanda shugaban NERC, Sunusi Garba ya sanya hannu, sabon farashin wutar lantarki da aka gindaya zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairu.

Hukumar ta ce za ta tabbatar da tsarin har sai an kara bayar da wani umarnin na daban, jaridar The Cable ta tabbatar.

KU KARANTA: Atiku ya siyar hannun jarinsa na Intel, ya dora laifi a kan gwamnatin Buhari

NERC ta ce dalilan da suka janyo karin kudin wutar sun hada da yadda farashin abubuwa suka karu a Najeriya, yanayin yadda darajar kudi ta zube, asarorin MDA, tsadar gas da sauransu.

Gwamnatin tarayya ta kara farashin wutar lantarki | Photo Source: Vanguard
Gwamnatin tarayya ta kara farashin wutar lantarki | Photo Source: Vanguard

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun yiwa Malami kisan gilla saboda ya kalubalanci garkuwa da mutane

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkar sojoji, Mohammed Ndume yace shugaba Muhammadu Buhari ya sauya dukkan ministocinsa da sauran jiga-jigai da ya nada, matsawar yana yi wa ‘yan Najeriya fatan alheri a 2021.

Duk da Ndume ya ce Buhari mutumin kirki ne, amma yana zagaye ne da wadanda basa fatan ganin cigaban Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sanata Ndume ya fadi hakan ne jiya, yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe