25.1 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

2023: Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna kasashen waje ta lashi takobin tara kudade don tallafawa Atiku a zabe mai gabatowa

Labarai2023: Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna kasashen waje ta lashi takobin tara kudade don tallafawa Atiku a zabe mai gabatowa
2c260f934a88dcf1

Wata kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, ga me da harkar siyasa mazauna kasar waje (DVND) ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, bayan ta sha alwashin tara kudade domin tallafawa. ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje sun kuma ce takarar Atiku ya kara musu kaimin son kada kuri’a a zabe mai zuwa.

Atiku shugabane a siyasance

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun babban darakta, T A Sule da mataimakin shugaban kungiyar,Anozie Ugenyi, kungiyar ta bayyana cewa a tarihi Atiku ya kasance shugaban a siyasa wanda duk wani mataki da furucinsa, ke nuna fahimtar manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Yana kulawa da lamarin mazauna kasar waje

A cewar kungiyar, Atiku ya nuna matukar kulawar sa ga abin da ke faruwa da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.
Kungiyar ta ci gaba da cewa:
Saboda haka ne muka yanke shawarar hada kan ‘yan uwanmu da ke gida domin su yi kokarin samun katinan su na zabe sannan kuma su fito don yin amfani da takardar shaidarsu domin tabbatar da kasa mai aminci, hadin kai da wadata.
“kuma mun, dauki nauyin tara kudaden da ake bukata don tallafawa wajen kamfen yayin da muke fatan wata rana za mu dawo cikin aminci, da hadin kai da wadata kasa.
“Abin farin ciki ne cewa mu da ke zaune a wasu ƙasashe muna tare da Atiku .
“Mun san cewa shugabanci irin nasa zai samar da cibiyoyin da ke da alhakin wannan niyya don tabbatar da hakkinmu na zabe.

Haka za ku cigaba da kwadago har ku mutu, Tinubu ga LP da PDP

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta tsaida ranar 16 ga watan Yuni a matsayin ranar zaben gwamnan jihar Osun, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola na fatan dawowa madafun iko a karo na biyu, yayin da Ademola Adeleke na PDP ya ke sahun gaba a gasar fidda gwamnan jihar.
Jam’iyyar LP ta tsaida Lasun Yusuf a matsayin ‘dan takarar gwamnanta.

Sai dai, Tinubu ya ce da kamar wuya PDP da LP su kai labari indai APC na takarar.

Yayin jawabi a zagayen kamfen, ya siffanta PDP da LP a matsayin “jam’iyyun lemar kwado.”
Ya bukaci jama’ar jihar Osun da su duba gaba abin da zai faru da su a taba su zabi APC.
Kada kuri’u yanzu yana hannunku. Ku zama masu lura. Ku kula. Baza kuyi haka a banza ba.

“Ku tuna da yaran ku sannan ku zabi wanda ya cancanta yadda gaba zata yi muku dadi. Ku fito da yawanku. Kada ku damu da PDP da sauran jam’iyyun lemar kwado – jam’iyyu irinsu Labour, zasu yi ta kwadago har su mutu gaba daya. Ubangiji bazai maisheku laburori ba.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe