28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Wata mata ta maka mijin ta a kotu saboda ya auro aminiyar ta a matsayin kishiya a gareta 

LabaraiAl'adaWata mata ta maka mijin ta a kotu saboda ya auro aminiyar ta a matsayin kishiya a gareta 

Wata mata matashiya ‘yar shekara 25 mai suna Firdausi Musa, ta maka tsohon mijin ta mai suna Saidu Abubakar a kotu, a garin Kaduna, saboda ya auro mata aminiyar kawar ta a matsayin kishiya. 

Da take bayani, lauyar mai karar, mai suna Zainab Murtala, ta ce, mijin matar ya kwashe kayan ta dake cikin akwati da sauran kyaututtukan da ya bata, duk ya mallakawa sabuwar amaryar ta sa. 

Wata mata ta maka mijin ta a kotu saboda ya auro aminiyar ta a matsayin kishiya a gareta

Auren matar bai dade ba

A cewar ta,

” Kwananan muka yi aure da shi, amma bamu tare a kowanne gida ba, tsawon wata biyu ke nan, kawai dai ya kama hotal ne, a can ne muke haduwa “. 

“Kwatsam sai ya ce, ya sake ni, daga baya ya mayar dani muka ci gaba da zama, sai ya sake saki na, inda daga nan sai ya auro kawata aminiya ta, kuma ya mallaka mata duk kayayyaki na, wanda ya hada har da dukkan kayan sawa ta”.

Ta fada 

Ta nemi kotu da ta dawo mata da kayan ta

Ta roki kotu da ta dawo mata da kayan ta, da aka kwashe mata, har ma da wadanda ta sanya kudin ta, ta siya yayin da taje Umarah a kasa mai tsarki. 

Firdausin ta kara da cewa, ita bata taba cewa mijin nata ya saketa ba. 

Mijin ya musanta ikirarin matar

A nasa bangaren, wanda ake kara, ta bakin lauyan sa mai suna Abubakar Sulaiman, ya musanta baiwa amaryar sa kayan da ya mallakawa Firdausin, a matsayin kyauta. 

Alkali Rilwanu Kyaudai, wanda shine ke sauraren karar, ya dage shariar zuwa tara ga watan Agusta, domin sake jin ta bakin wanda ake kara.

Yadda na dawo da budurwar mijina gidana don mu ci gaba da faranta masa rai tare, Matar aure

Wasu mata biyu a kasar Kenya sun bayyana yadda yanzu haka suke zama a gida daya tare da mijinsu, Abraham, Legit.ng ta ruwaito.

Sarah da Maureen suna zama ne a matsayin kishiyoyi bayan Abraham ya auresu gaba daya, kuma suna nuna wa juna so da kauna tamkar ‘yan uwa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe