Demi Minor mai shekaru 27 ya koma bangaren gidan gyaran halin Garden State Youth daga Edna Mahan a watan Yuni. An daure ta ne bayan tayi yunkurin rataye kanta yayin da ta koma GSCF, Daily Mail ta ruwaito.
A wata wallafa, ta bayyana cewa ma’aikatan gidan gyaran halin sun sa mata ido yayin da aka umarce ta tube don wata mace ta duba ta.
A wata wallafar ta daban, ta ce an yi mata dukan tsiya. Ita din dama ta sauya jinsinta ne daga namiji zuwa mace wanda hakan yasa aka daureta a bangaren mata. Daga nan kuma ta dirkawa mata biyu ciki.
An yi mata daurin shekaru 30 ne bayan ta yi yunkurin halaka marikinta, daga nan aka mayar da ita bangaren maza maimakon bangaren matan da da farko take a watan Yuni.
A cewarta, yayin da take tsare a firzin din New Jersy State, ana ta kiranta da gardi fiye da sau 30.
Ta yi fice ne a gidan gyaran halin bayan ya dirkawa mata har biyu ciki. Kamar ta rubuta a takarda:
“Na yarda an ajiye ni a bangaren maza amma ba zan taba yarda da cewa ni ba tamace bace.”
Ta ce ana cutar da ita sosai kuma tana fuskantar tsana tsakaninta da abokan zaman ta na gidan gyaran halin.
Ta ce wannan lamarin na iya janyo ta rasa ranta saboda cutarwar da take fuskanta ta wuce gona da iri.
Yadda wani namiji wanda ya koma mace ya dirka wa mata 2 ciki a gidan yarin mata zalla
Wani da aka haifa a matsayin namiji wanda daga bisani ya koma mace ya dirkawa wasu matan gidan yarin da yake ciki juna biyu, kasancewar an killacesu tare.
Wasu mata guda biyu a gidan yarin New Jersey sun dauki ciki bayan sun amince da lalata da wani da ya koma mace, shafin Instablog ya ruwaito.
Washington Times ta ruwaito yadda aka killace matan a asibitin gyaran hali na Edna Mahan.
Dan Sperrazza, kakakin sashin mata na New Jersey na gyaran hali, ya bayyana wa NJ.com yadda matan suke dauke da juna biyu bayan sun “amince da yin lalata da wani da ya koma mace.
“Demi Minor ta amince da zama wacce ke da alhakin dirka wa fursinonin ciki, ta wani shafi Justice 4 Demi, wanda take kula da shi daga gidan yarin da take.
Shafin labaran ya ruwaito yadda gidan yarin ya kunshi fursunoni 27 wadanda aka haifa a maza, amma daga baya suka koma mata.
An maidasu gidan yarin ne a shekarar 2019 bayan shigar da karar da ACLU tayi, bayan wata mata da aka haifa namiji ta fuskanci cin zarafi daga gidan yarin maza.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com