23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Sama da ƴan bindiga 100 ne suka halarci bikin nadin sarautar shugabansu da aka yi a jihar Zamfara

LabaraiSama da ƴan bindiga 100 ne suka halarci bikin nadin sarautar shugabansu da aka yi a jihar Zamfara

Sama da ƴan bindiga 100, a ranar Asabar, suka halarci naɗin sarautar wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga mai suna Ada Aleru a matsayin Sarkin Fulani wacce sarkin Yandoto yayi masa.

Ƴan bindigan sun yi gungu wurin halartar naɗin shugaban na su

Mutane a garin Tsafe jihar Zamfara sun ce ƴan bindigan sama da 100 sun halarci naɗin sarautar shugaban na su wacce sarkin Yandoto yayi masa.

Wata majiya ta bayyana cewa:

Ƴan bindigan sun taho akan babura ba tare da bindigun su ba, ƙaramin biki ne wanda mutane ƙalilan suka halarta.

Sarkin Yandoto, Alhaji Garba Marafa, ya ba da sarautar Sarki Fulani ga ƙasurgumin ɗan bindigan wanda yake kai hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina saboda yana son ya rungumi yin sulhu.

A wani zama da akayi, Ada Aleru, ya yarda ya daina kai hare-hare ga mutanen ƙauyukan dake a masarautar. Ya kuma yarda ya bar mutane suje gonakin su.

Hakan ya sanya masarautar tayi naɗin sarautar ga Aleru, domin taimakawa wurin ganin zaman lafiya ya dawo a masarautar.

Naɗin sarautar da akayi wa ƙasurgumin shugaban ƴan bindigan, ya jawo cece-kuce sosai, ganin yadda jihar ke fama da matsalolin tsaro, sannan yana cikin waɗanda aƙe nema ruwa a jallo.

Gwamna Matawalle ya dakatar da Sarkin da ya bawa kasurgumin dan bindiga sarauta a jihar Zamfara

A wani labari na daban kuma, Gwamna Matawalle ya dakatar da sarkin da ya naɗa ƙasurgumin ɗan bindiga sarauta a jihar.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da Sarkin Birnin ‘Yandoto, Aliyu Marafa, bisa bada sarautar Sarkin Fulani ga wani shugaban ‘yan fashi da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero.

Matakin da Masarautar ta dauka ya jawo kace nace, inda jama’a da dama suka yi Allah-wadai da irin wannan lamari na karrama masu aikata laifuka.

Sai dai a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe ya fitar, gwamnatin ta nesanta kanta daga matakin da sarkin ya dauka,inda ta dakatar da shi tare da kafa kwamitin binciki game da lamarin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe