23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Mune muka kashe tsoho dan shekara 90 muka kona gawarsa kuma muka sace kudi N430,000.00 – Inji wasu matasan yan ta’adda 

LabaraiMune muka kashe tsoho dan shekara 90 muka kona gawarsa kuma muka sace kudi N430,000.00 - Inji wasu matasan yan ta'adda 

Hukumar rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto tayi nasarar cafke wadansu bata gari da ake zargin yan wata kungiyar sa kai ne, da laifin kashewa tare da kone wani tsoho dan shekara 90. A rahoton TVC News. 

 TVC News din, ta tabbatarda cewa abin ya faru ne a kauyen Zangon Atti dake  karamar hukumar Gwadabawa ta jihar. 

kashe tsoho
Mune muka kashe tsoho dan shekara 90 muka kona gawarsa kuma muka sace kudi N430,000.00

Yadda suka kashe tsohon

Yan ta’addan, sun hilaci tsohon mai suna Muhammad Riskuwa ne shi da dansa Shehu Mamman, bayan sun dauke su da hira, sai daya daga cikin su ya harbe tsohon har lahira. 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sanusi Abubakar, ya ce masu laifin sun amsa laifin kashe tsohon, sannan sun amsa bincike gidan tsohon, inda suka yi awun gaba da kudade kimanin Naira dubu dari hudu da talatin N430,000.00 . bayan sun kone gawar mutumin. 

Jami’in ya kara da cewa za’a gurfanar da masu laifin a gaban kotu, da zarar an kammala bincike.

Kotu ta yanke wa wata ‘yar aiki hukuncin kisa bisa laifin kashe mahaifiyar tsohon gwamna jihar Edo

Birnin Benin, jihar Edo – An yanke wa Miss Dominion Okoro, ‘yar aiki mai shekaru 25 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Madam Maria Oredola Igbinedion, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Edo, Cif Lucky Igbinedion. Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Mai shari’a Efe Ikponmwoba na wata babbar kotun jihar Edo shi ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 21 ga watan Yuni.

Ta yi amfani da kujera wajen kashe marigayiyar

Rahotanni sun bayyana cewa an samu ‘yar aikin da laifin kashe Madam Igbinedion mai shekaru 85 in da aka gano cewar tayi amfani da kujera ne wajen aikata laifin da niyyar yi mata fashin kudi N100,000 a ranar 1 ga watan Disamba, 2021, a gidanta dake Ugbor, cikin birnin Benin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe