31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Mijina lusari ne ya ɓoye a banɗaki ya barni a hannun ƴan fashi -Matar aure ta nemi kotu ta raba auren su

LabaraiMijina lusari ne ya ɓoye a banɗaki ya barni a hannun ƴan fashi -Matar aure ta nemi kotu ta raba auren su

Wata matar aure mai suna Asiata Oladejo ta shaidawa wata kotu a birnin Ibadan, jihar Oyo, ta raba aurenta da mijinta, Abidemi, saboda ragon namiji ne domin ya gudu ya bar ta da yaran su a hannun ƴan fashi da makami.

Ta bayyana yadda mijin nata ya ɓoye

Shafin Yabaleftonline ya tattaro cewa Oladejo ta bayyana hakan ne lokacin da take mayar da bayani kan ƙarar da mijinta ya shigar.

Mai girma mai shari’a, har yanzu ban gama farfaɗowa daga firgicin da na shiga ba lokacin da gungun ɓarayi suka faɗo mana gida. Ya ɓoye a cikin banɗaki, inda ya bar ni a hannun ƴan fashi da makamin waɗanda suka firgita dukkanin mutanen gida.

Mai girma mai shari’a, lokacin da ɓarayin suka zo misalin ƙarfe 1 na dare. Mijina yayi ɓatan dabo an neme shi an rasa domin ya kare yaran da ni.

Ban sani ba ashe ya ɓoye a banɗaki. Sai da suka tafi sannan ya fito. Mijina yana son mu cigaba da zama a wannan gidan. A cewar ta

Ya amsa cewa ya ɓoye a banɗaki


Da yake kare kansa, Abidemi yace matar tasa ta cika saurin fushi.

Tana zuwan min shago hakanan kawai ta ci zarafi na. Eh da gaske ne na ɓoye a banɗaki lokacin da ƴan fashi da makami suka zo mana gida. Duk wani ƙoƙarin dawoɓda ita ɗakin ta yaci tura saboda tace tana jin tsoro har yanzu.

Ya nemi kotu da bashi damar kula da yaran sa guda uku saboda yana sauke haƙƙin sa a matsayin sa na uba.

Da take yanke hukunci, mai shari’a Mrs S. M. akintayo, ta amsa roƙon mai ƙarar na hana Oladejo, yin barazana, cin zarafi da shiga cikin rayuwar rayuwar Abidemi.

Yadda na ritsa mijina yana lalata da mata 8 akan gadon aurenmu, Matar aure

A wani labarin kuma wata matar aure ta bayyana yadda ta ritsa mijinta yana lalata da mata a gadon su na aure.

Wata mata wacce muryarta ta dinga yawo a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a kwanakin baya inda ‘yan mata su ka dinga hawa muryarta ta bayyana yadda ta ritsa mijinta da mata 8 akan gadon aurensu.

Kamar yadda bidiyon wanda shafin lucky Udu ya wallafa a Facebook, an ji yadda matar take bayani dalla-dalla inda tace an samu wannan muryar tata ne a jawabin da tayi a kotu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe