27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Sabbin hotuna da bidiyon jaruma Rahama Sadau a lokacin da take holewa ita da ‘yan uwan ta a kasar Cyprus 

LabaraiSabbin hotuna da bidiyon jaruma Rahama Sadau a lokacin da take holewa ita da 'yan uwan ta a kasar Cyprus 

Shahararriyar Jarumar finafinan Hausa, Rahama Sadau, ta fitar da wani bidiyo gami da hotuna, wandanda suka dauka ita da yan uwanta ta a kasar Cyprus yayin da suka je yawon shakatawa. 

Rahama ta walla sabbin hotuna da bidiyo a shafinta na instagram

 Jarumar ta wallafa hotunan ne a shafin ta na instagram, wanda suka ja hankalin masu kallo da sharhi kan hotunan da ta fito a ciki  wadansu irin salo. 

Bugu da kari, jaruma Rahamar tana nunawa yan uwan nata Soyayya, ta yadda take yin duk wani abu da zata iya yi, domin sanya musu farin ciki a koda yaushe. 

Ga hotunan Rahama sadau wanda suka dauka a kasar Cyprus a kasa

rahama sadau
rahama sadau
rahama sadau
rahama sadau
rahama sadau

Daga bidiyon da ta yada kuwa, jaruma Rahamar ta bayyana cikin annashuwa tare da farin ciki  a cikin yan uwan nata inda suka dinga shakatawa da juna, a wani yanki  mai suna   Kyrenia District, wanda  daya ne daga cikin manyan yankunan kasar Cyprus. 

Wannan bidiyo da hotunan Rahama, sun ja Hankulan mutane a kafafen sadarwa, inda masu sharhi da dama suka tofa albarkacin bakin su.

Daga gida ake fara samun tarbiyya, Inji Rahama Sadau

Sau da yawa akan ce wasu jaruman Kannywood suna yin wasu abubuwan da gayya don a dinga cece-kuce akansu wanda wasu ke ganin hakan ne kasuwancinsu.

Wasu na ganin idan har ba a maganar jaruman, kasuwarsu ta mutu. Hakan ke sa wani lokacin da kura ta lafa sai su kara taya da sabuwa bayan wani dan lokaci, Tsakar Gida ta ruwaito.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe