24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

An kama mutumin da ya kaiwa likita farmaki da gatari a Bauchi

LabaraiAn kama mutumin da ya kaiwa likita farmaki da gatari a Bauchi

‘Yan sandan jihar Bauchi sun yi ram da wani mutum bayan ya kai wa wani likita farmaki a Babban asibitin Misau da gatari akan an samu tangarda yayin bai wa ‘yar uwarsa kula yayin da take nakuda, Linda Ikeji ta ruwaito.

Yayin bayyanawa manema labarai, shugaban kungiyar likitoci ta jihar, Adamu Sambo ya ce kawun marar lafiyar yayin da aka amshi haihuwar jaririnta ya kai wa Sani farmakin.

“Abinda ya faru shi ne mara lafiyar ta je asibitin bayan ko dai an turo ta daga asibitin kudi ko kuma sun je dakansu, amma dai ta yi nakuda mai tsawo. Kuma wannan ne haihuwarta na farko amma aka boyewa asibiti. Ta jigata daga inda aka turo ta.

“Bayan an gama dubata, an fahimci cewa kan yarinyar ya juye kuma mai nakudar bata da karfin da zata haihu dakanta

“Bayan ta haihu an samu matsala don sai da ta yage wanda aka mayar aka dinke ta amma duk da haka ta ci gaba da zub da jini.”


Sambo ya bayyana cewa ganin hakan ne yasa aka tura ta babban asibitin jihar da ke Azare, Katagum don a ci gaba da kulawa da ita.

“Abin ban takaicin shine ya kai farmakin ne ga wanda ba ya cikin wadanda su ka duba mara lafiyar ya dauki gatari ya sare shi har sau hudu. Yanzu haka yana asibiti ana kulawa da shi,” a cewarsa.

‘Yan bindiga sun kai wa tawagar Shugaba Buhari farmaki a Katsina, mutum 2 sun jigata

‘Yan ta’adda masu tain yawa da ke addabar jiha Katsina da kewaye sun kai mummunan farmaki kan tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta hallara a jihar Katsina kafin bikin babbar sallah.

Tawagar motocin dake dauke da jami’an tsaro, ‘yan jaridar gidan gwamnati da sauransu ta fuskanci farmakin ne a Dustinma, jihar Katsina, da yammacin ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Mutum biyu sun samu aunika sakamakon farmakin da fadar shugaban kasa ta kwatanta da kwanton bauna.

Lamarin ya faru ne kafn zuwan shugaban kasan Daura a ranar Laraba domin yin shagalin bikin babbar sallah a ranar Asabar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe