26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Hotunan tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa, da matashin da tayi wuff da shi

LabaraiHotunan tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa, da matashin da tayi wuff da shi

Hoton Hajiya Hauwa, matar tsohon gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai, da matashin mijinta, Haliru Saad Malami, da tayi wuff da shi, LIB ta ruwaito.

An samu hotunan ne bayan wani mai hoto Nexus, wanda ya wallafa a ranar Talata, 12 ga watan Yuli.

Hauwa ta auri Malami, wanda shi ne mai kamfanin ITBAN Global Resources LTd, a 2019, bayan shekaru biyu da mutuwar Suntai.

Hauwa ta kai shekaru 50 da doriya da haihuwa yayin da mijinta ya ke da shekaru 30 da doriya, kuma ‘yar uwa ce ga Turai Yar’Adua, matar tsohon shugaban kasa Umaru Yar’Adua.

Idan ba a manta ba, Suntai ya tafka hatsarin jirgin sama a Yola a shekarar 2012, sannan aka zarce da shi kasar waje don a duba lafiyarsa.

Ya mutu ranar 28 ga watan Yunin 2017, a Houston, Texas, Amurka bayan fama da ciwo akan hatsarin jirgin saman da yayi.

Wani mutum ya halaka tsohuwa ƴar shekara 71, ya sayar da sassan jikin ta kan N22,200

Hukumar ƴan sanda a jihar Ogun, ta cafke wani mai suna Dauda Bello, mai shekaru 54, bisa zargin halaka wata tsohuwa Mrs Mesesi Adisa, mai shekaru 71 a duniya.

Dauda kuma ya yanke wuyan hannaye da idon guiwoyin matar sannan ya sayar da su ga wani akan kuɗi N22,200. Ƴan sanda sun shaida cewa wanda ya siya sassan jikin ya arce. Jaridar The Nation ta rahoto.

Ya shiga hannun hukuma

An dai cafke wanda ake zargin ne a ranar 7 ga watan Yuni, 2022 bayan ɓatan Mrs Adisa kwanaki kaɗan bayan ta bar gida.

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fada a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ƴan’uwan tsohuwar sun shigar da rahoton ɓacewar mutum a ofishin ƴan sanda na Sabo-Ilupeju.

Wanda ake zargin na safarar ƙananan yara tare da tsohuwar


Oyeyemi yace wanda ake zargin ya amsa cewa ya san matar, inda yace su dukan su suna harƙallar safarar ƙananan yara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe