28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Mafi yawanci matan da suke neman maza a waje ba mutanen banza bane saboda wadannan  dalilai nawa – Inji Blessing Okoro

LabaraiMafi yawanci matan da suke neman maza a waje ba mutanen banza bane saboda wadannan  dalilai nawa - Inji Blessing Okoro

Shahararriyar masaniyar ilimin zamantakewa, Blessing Okoro Nkiruka, ta ce mafi yawan mata wadanda suke neman maza a waje ba wai mutanen banza bane, kamar yadda ake daukar su a cikin al’umma. 

Da take magana a wani bidiyo, Blessing din ta bayyana wadansu dalilai da suke nuna cewa masu waccan halayyar, ba fa mutanen banza bane. 

neman maza
Mafi yawanci matan da suke neman maza ba mutanen banza bane saboda wadannan  dalilai nawa

Dalilan da ta fada gasu kamar haka 

A cewar ta, mafi yawancin mata, basu da ilimi akan menene shakuwa, kuma yaya ake samun shakuwa da masoyi. Sabo da haka akwai wadanda suke da tunanin cewa, har sai wane ya sadu da sune, sannan zasu sami Soyayya da shakuwa ta musamman daga gareshi. 

Ta kara da cewa, bawai suna neman mazaje barkatai domin sun sha giya sun bugu bane, ba kuma wai domin su karbi kudi daga garesu ba ne, a’a suna neman mazan ne domin  suna da wancan tunani na cewa ana samun shakuwar Soyayya ta gaskiya ne kadai ta hanyar saduwa, saboda haka suna neman soyayyar gaskiya ne. 

Babban kuskuren da matan masu neman maza keyi

Amma kuma, a kokarin su na neman Soyayya ta gaskiya, sai suke yin wani kuskure, na saurin bayar da kansu, wanda kuma daga baya sai aci moriyar ganga kuma a yar da kwauren ta. Sai mazan su yi amfani da su, kuma su tsere su bar su. 

Daga karshe ta shawarci matan da su dena bayyana dukkanin halin da suke ciki ga mazan da suka nuna sha’awar auren su.

Kaso 98% na mazan Najeriya masu aure, su na da ‘yan matansu a waje, Boma

Jarumin shirin gida talabijin na BBNaija, Boma Akpore ya ce kaso 98 bisa dari na mazan aure da ke kasar Najeriya su na da ‘yan matansu a waje baya ga matansu na aure, LIB ta ruwaito.

Boma ya bayyana hakan ne a wani shirin taron BBNaija na “Shine Ya Eye” wanda aka bayyana ranar 16 ga watan Yunin 2022.

Kamar yadda yace:

“Kaso 95% na mazan Najeriya masu aure suna da ‘yan matansy a waje, kila ma kaso 98.

“Zan fadi abinda mutane dayawa suke tsoron fadi. Kaso 98% na mazan Najeriya masu aure suna da ‘yan mata. Wa kuke tunanin yana daukar nauyin ‘yan matan?

“Kusan ko wanne namiji mai aure yana da budurwarsa. Duk ‘yan mata nan, abubuwan da suke siya duk maza masu aure ne ke siya musu.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe