26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Shugaba Buhari ya bayyana dalilan da yasa ya kulle iyakokin ƙasar nan

LabaraiShugaba Buhari ya bayyana dalilan da yasa ya kulle iyakokin ƙasar nan

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a a mahaifar sa ta Daura ya bayyana cewa ya yanke shawarar kulle iyakokin ƙasar nan ne domin amfanin manoma.

Shugaba Buhari ya jinjinawa manoma

Shugaba Buhari kuma ya yaba ga manoman ƙasar nan bisa samar da shinkafar da baa taɓa samu ba da sauran kayayyakin abinci, inda ya nuna gamsuwar sa kan cewa shirye-shiryen gwamnatin sa kan aikin noma na haifar da ɗa mai ido. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Buhari yace gwamnatin sa ta ɗauki matakai da dama ciki har da kulle iyakokin ƙasar nan na ƙasa har na tsawon shekara biyu domin amfanin manoma waɗanda sune akan gaba wurin tafiyar da tattalin arziƙin ƙauyuka, inda ya nuna jindaɗin sa kan cewa hakan yayi amfani yadda yakamata ga ƙasar nan.

Dole a noma abinda zaa ci ƙasa

Da yake magana ga zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar Katsina da suka je masa yawon sallah, shugaba Buhari yace:

Ina da fahimta sosai akan ƙasar nan da mutanen ta. Hakan ya sanya muka kawo waɗannan shirye-shiryen kan noma. Na ce dole mu noma abinda muke ci sannan mu ci abinda muka noma.

Wannan ƙasa ce wacce a da take dogaro ga shinkafa ƴar ƙasar waje. Mun kulle iyakar ƙasar nan ta shigowa da shinkafar ƙasar waje. Na ce meyasa ba zamu ci shinkafa ƴar Najeriya ba, da tsare-tsaren da muka sanya a ƙasa, ƴan Najeriya na cin shinkafa ƴar gida.

Shugaba Buhari ya aike da wani muhimman saƙo ga matasan Najeriya

A wani labari na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike wa matasan Najeriya da wani muhimmin saƙo. Shugaban ya jawo hankalin matasan ƙasar nan kan cewa da su tashi tsaye su nemi na kan su domin babu sauran aikin gwamnati a ƙasar nan.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya roƙi matasa da su nemi ilmi ba domin samun aikin gwamnati ba saboda yanzu ba sauran ayyuka a gwamnati.

Ya kuma roƙi matasan da su samu sanin tarihi saboda kada su sake yin irin kurakuran da na baya suka yi. Jaridar The Punch ta rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe